Ina tare da bangaren Giadom, shine shugaban APC a yanzu – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayan sa ga shugabancin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Kudu-Maso-Kudu, Victor Giadom.

Kakakin fadar shugaban Kasa, Garba Shehu ya sanar da haka a takarda da ya fitar ranar Laraba.

” Buhari zai halarci taron jam’iyyar wanda Giadom ya kira saboda shine yanzu shugaban jam’iyyar, kamar yadda kotu ta yanke hukunci.

” Kwararru sun ba shugaba Buhari shawara mai zurfi game da badakalar shugabancin jam’iyyar a yanzu. Kuma yabi wannan shawara da khudubobin su dalla-dalla. A karshe dai hankalin sa ya fi kwanciya kan shugabancin Giadom a matsayin shugaban jam’iyyar na wucin gadi bisa hukuncin kotu.

Kamar yadda Shehu ya fadi, ana sa ran shugabannin jam’iyyar, gwamnoni da ‘yan majalisu za su halarci wannan taro.

Kotu ta yanke hukuncin Giadom ne shugaban jam’iyyar na tsawon makonni biyu da za su zo. Amma kuma jam’iyyar ta garzaya kotu ita ma inda ta sa kotu ta ba da izinin jingine hukuncin wancan kotun.

Giadom dai ya lashi takobin lallai shine shugaban jam’iyyar APC a yanzu.

Idan ba a manta ba kotun daukaka kara ta dakatar da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole daga jam’iyyar a dalilin hukuncin dakatar da shi da kotu ta yi a baya.

Tun daga mazabar sa da karabar hukumar sa ta Etsako West wakilan jam’iyyar suka dakatar da shi wanda hakan ya ba kotun daukaka kara daman jaddada hukuncin dakatar da shi da kotu ta yi.

Duka da cewa jam’iyyar ta rattaba hannu cewa sanata Abiola Ajimobi ne shugaban ta na rikon kwarya, Giadom ya yi watsi da jam’iyyar ya nada kansa shugaban jam’iyyar na wucin gadi.

Share.

game da Author