COVID-19: Siyasar baddala alkaluman adadin masu dauke da cutar, Daga Jibrin Ibrahim

0

Tun da farko yaki, fahimta da kuma kaffa-kaffa da cutar Coronavirus sun ginu ne a kan rukunai uku: Tsoratar da al’umma dangane da irin mummunar illar cutar; rashin daukar ta muhimmanci a wani bangare; sai kuma yadda mutane suka shashantar da kan su wajen kin gaskata cewa cutar tabbas akwai ta.

An rika fargabar cewa Coronavirus za ta iya yin irin mummunan kisan da annobar 1918 ta yi a duniya, inda cikin shekara daya ta kama mutum milyan 500, kuma ta kashe sama da mutum milyan 50.

Daga nan aka rika cusa wa jama’a tsoro, ana garkame su a cikin gidajen su. Ya kasance mai hali da fakiri kowa na gida. Babu maganar fita.

Shi kuwa talaka idan ka kulle shi a gida, yunwa ce za ta fitine shi. Daga yunwa kuwa to ya kai makura kenan. Daga inda ka ce wa fakiri kada ya fita neman, to tamkar ka kwace dan abincin da ke hannun sa ne.

Bayan an kulle fakirai, Gwamnatin Tarayya ta rika bi ta na bayar da tallafin da bai fi cikin tafin hannu ba. Dan abincin nan da za a iya kira ci-kada-ka-mutu ko kuma ka-ki-ci-ka-mutu.

Ko ma dai me kenan, nan da shekaru masu yawa za mu rika bibiya da nazarin yadda kulle mutane a gida saboda Coronavirus ya haifar da yunwa, talauci, kassara al’umma, tattalin arziki da sauran su.

Bayan gwamnatin tarayya ta yi na ta kokarin ta gaji, sai kuma ta maida shirin dakile cutar Coronavirus kacokan a hannun gwamnonin jihohi. Sai ya kasance shi kan sa Kwamitin Dakile Cutar Coronavirus na Shugaban Kasa da Hukumar Yaki Da Cututtuka ta Kasa (NCDC), duk suka koma dogaro da sakamakon da Gwamnonin Jihohi ke ba su, wajen sanin adadin wadanda suka kamu, wadanda suka wartsake da kuma wadanda Coronavirus ta kashe a kasar nan.

Daga lokacin da aka maida al’amurra a hannun gwamnoni, idan ka debe Lagos da wasu jihohi biyu haka, za ka ga sauran jihohin duk adadin masu kamuwa ya na raguwa.

Ba wani abu ne ya haifar sa hakan ba, sai kawai gwamnonin ba su so ana alakanta jihohin su da cutar.

Saboda haka a halin da ake ciki, jihohi da dama na siyasantar da adadin alkaluman wadanda cutar Coronavirus ta kama, su na rage adadin, don kada a kyamaci jihar su.

Sun fi so su saki mutane kowa ya fito domin a ci gaba da Harkokin yau da kullum a jihohin su.

Gwamnoni Da Siyasar COVID-19:

A yanzu gwamna ke kafa Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus a jihar sa.

Sannan kuma kowane gwamna ke kafa Kwamitin gwajin cutar Coronavirus.

Gwamna ne ya nada su domin su tattara gwajin da suke yi.

Wannan kwamiti ke da alhakin bayar da samfuri din gwaji ga hukumar NCDC.

Wannan kwamiti sai adadin da ya ga dama zai mika na samfurin gwaji.

Don haka idan ya mika samfur na mutane da yawa, to tabbas za a samu adadin wadanda suka kamu da yawa.

Idan kuma jiha ta bayar da adadin gwaji kalilan, to wadanda za a samu sun kamu a jihar ba su da yawa kenan.

Tunda kuwa gwamnoni ba su so a rika kallon jihar su jihar Coronavirus, to kuwa na za su rika yin gwajin mutane masu yawa na kenan.

Ba abin mamaki ba ne da Shugaban Kungiyar Likitoci ta NMA, Farfesa Inmocent Ujah ya yi kakkausan gargadi a kan gwamnoni ba a ranar Litinin, a Gidan Talbijin na Channels.

Cewa ya yi, “Najeriya za ta shiga mummunan garari muddin aka bar shirin yaki da cutar Coronavirus a hannun gwamnoni.”

Mu dauki yadda a yanzu a jihar Kano ake ta samun karancin adadin masu kamuwa da cutar a kullum.

Amma kuma Shugaban Cibiyar Yaki da Cututtaka ta Jami’ar Bayero, Isa Hashim ya tabbatar da cewa karancin adadin masu kamuwa da cutar a Kano a yanzu, ba ya na nufin cutar na raguwa ba ce a Kano.

Ya ce adadin na raguwa ne saboda kawai ba a kai samfuri na gwajin da aka dauka daga jikin mutane domin a auna su.

A yanzu dai an bude kofa a fita, a ci gaba da harkoki, gwamnati ta yi bakin na ta kokarin. Kowa kawai ta sa ta fisshe shi kenan.

Ya rage ga wanda ya ji gargadi ya dauki matakan kare kan sa da kan sa. Su kuma gwamnoni sai adadin da suka ga dama za a gwada. Sai adadin da suka ga dama za a kai samfur. Kuma sai adadin da suka ga dama za a ce sun kamu.

Masana da dama sun yi kirdadon cewa kafin wannan cuta ta rabu da mu, watakila a kai watanni shida nan gaba. Saura da me? Duk wanda bai ji bari ba, to zai ji hoho.

Farfesa Jibrin Shi Ne Shugaban Hukumar Gudanarwar Editocin PREMIUM TIMES.

Share.

game da Author