A cikin watan Mayu ne Joseph Osuigwe dake da shekaru 35 ya gano cewa baya jin kamshin da dandanon girkin abincin matarsa.
Haka kazalika idan ya saka turare ba ya jin kamshin turaren kwatakwata. Osuigwe ya ce da ya ga haka sai ya siyo man zafi ya shafa a hancinsa inda shima bai ji koma ba.
Haka kuma a watan Afrilu Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa rashin jin dandanon abinci da rashin jin kamshi na daga ciki alamun kamuwa da cutar Korona.
A makon da WHO ta fitar da wannan bayanai mutane a Najeriya suka rika yin kukan samun irin wannan matsaloli na rashin jin Kamshi da dandano a baki.
Haka kuma wani Tunde Ajayi shima a shafinsa na twitter ya ce idan mutum na fama da irin wadannan alamu a jikinsa ya latsa shaidar ‘Ina so’ wato ‘Like’.
Cikin lokaci kadan mutane sama da 3,300 suka latsa haka cewa suna fama da haka.
Osuigwe ya fahimci cewa kamar akwai alamun ya kamu da cutar Covid-19 inda ya garzaya asibiti domin a yi masa gwajin cutar.
Da ya je asibiti Sai ma’aikatan kiwon lafiya su ka ce masa baya bukatan yin gwajin cutar cewa alamun da yake ji a jikin sa ba su da yanayi da ya kamu da kwayoyin cutar Korona.
“Da na dage sai an yi mun gwajin cutar ne ma’aikatan kiwon lafiya suka yi min gwajin cutar duk da ba su so. Sakamakon gwajin sai ya nuna ashe ya kamu da cutar.
Ba dole bane idan ana fama da rashin jin dandano da rashin jin kamsh shike nan kuma wai an kamu da Korona kenan.
Rashin jin kamshi da dandanon abinci ya ta da hankalin mutane da dama a Najeriya da duniya gaba daya.
Likitoci dake ‘American Academy’ sun bayyana cewa mutanen da suka kamu da cutar amma basu nuna alamu cutar Covid-19 a jikin su kuma basu jin kamshi ko dandanon abinci sun kara yawa a duniya.
A kasar Korea kashi 30 daga cikin mutum 2,000 da suka kamu da coronavirus na fama da wannan matsala.
Wasu ma’aikatan kiwon lafiya sun ce ba lallai bane idan mutum baya jin dandano ko kamshi abinci shikenan sai a ce ya kamu da da Covid-19.
Domin akwai wanda zai nuna irin wadannan alamu amma kuma bashi dauke da kwayoyin cutar coronavirus.
Sun ce yin gwajin cutar ne kadai hanyar da zai sa a gane ko mutum na da shi ko bashi da shi.
Wani shi kuma mai suna Valentine Osondu dake zama a Abuja ya ce sakamakon gwajin da ya yi ya nuna cewa ya kamu da zazzabin cizon sauro a lokacin da ya rasa jin kamshi da dandanon abinci.
Osondu ya ce ya yi sati daya yana shan maganin zazzabi cizon sauro amma bai samu sauki ba.
“Wani abokina ya bani shawarar na dafa citta, tafarnuwa da lemun tsami na rika shan ruwa duk safe, haka Allah yayi na samu sauki.
Inganta yin gwajin cutar a Najeriya
Korafe-korafen da mutane suka yi game da wadannan alamu ya sa Hukumar NCDC ta hada wadannan alamu cikin sauran jerin alamun kamuwa da Korona.
“Idan mutum na fama da rashin jin kamshi ko dandanon abinci,ciwon kai da yoyon hanci ya hanzarta zuwa asibiti domin a yi masa gwajin cutar Korona tunda wuri.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya Hukumar NCDC ta ce burinta shine ta yi wa mutum miliyan biyu gwajin cutar a cikin watanni uku.
A yanzu haka NCDC na yi wa mutum 900 zuwa 1,400 gwajin cutar a duk rana a wuraren yin gwajin cutar 26 dake fadin kasar nan.
A takaice dai mutum 115,760 aka yi wa gwajin cutar daga cikin ‘yan Najeriya sama da miliyan 200 dake kasar nan.
Daga ciki mutum 20,000 sa suka Kamu da cutar, an sallami sama da 7,000 sannan sama da mutum 500 sun mutu.
Shan magani ba tare da izinin Likita ba
Da dama dake fama da irin wadannan alamu a jikin su na shan magani ba tare da Likita ya duba su ba.
Hukumar NCDC ta yi kira ga mutane da su guji shan magani ba tare da izinin Likita ba domin yin haka na cutar da lafiyar mutum.
A yanzu dai duk mai fama da matsalar rashin jin kamshin ko dandanon abinci zai dafa citta, tafarnuwa da lemun tsami ya sha ruwan duk safe ko kuma su Sha Maganin zazzabi cizon sauro ‘Chloroquine’ ko kuma hydroxychloroquine’ kuma duk sun samu sauki.
Mafita
A tsokacin da yayi Shugaban likitocin NARD reshen Abuja Roland Aigbovo ya ce kamata ya yi gwamnati ta kara yawan wuraren gwajin cutar a manyan asibitocin kasar nan.