Dole manoma su zage damtse bana, gwamnati bata da kudin shigo da abinci daga waje – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga manoman Najeriya su dage wajen noma abinci a wannan shekara domin gwamnati ba ta da kudin shigo da abinci daga waje.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban Kasa bayan ya sakko daga sallar Idi, da yayi a Aso Rock.

” Ina fatan a samu damina mai albarka domin albarkatun gona su yi kyau su yalwata a bana. Ina kuma fatan manoma zasu koma gona su dukufa da aiki domin noma abincin da muke bukata a kasar nan. Domin kuwa babu kudin da zamu shigo da abinci daga waje. Dole mu noma abincin da zamu ci bana.

Tun kafin barkewar annobar coronavirus, Najeriya ta rufe iyakokin ta da wasu kasashen domin hana shigo da kayan abinci kamar su shinkafa, Kaji da man fetur.

A dalilin Korona kuma kasar ta rufe duka iyakokinta har ga mutane, amma duk da haka a kan hada baki da baragurbin Jami’an tsaro ana harkallar shigo da iren-iren wadannan kaya cikin kasar nan.

Bayan haka Shugaba Buhari ya gargadi ‘yan Najeriya su rika bin dokokin ma’aikatar kiwon Lafiya game da annobar Korona.

” Ku duba dai ku gani, da mu kasashe masu tasowa da kashen da suka ci gaba Korana ta dagula mana komai. Kowa ya fada cikin halin kunci da damuwa a dalilin cutar. Gara mu ma, annobar bata yi mana caccakar da ta yi wa wasu kasashen ba.

Idan ba a manta ba a makon jiya, ministan kudi, Zainab Ahmed ta bayyana cewa Babu makawa sai Najeriya ta fada cikin halin tabarbarewar tattalin arziki.

Najeriya kasa ce da ta dogara kacokan Kan man fetur. A sanadiyyar annobar Korona, farashin man fetur ya ruguje matuka kuma ga annobar Korona.

Najeriya ta na ta kashe magudan kudaden ta wajen yaki da yaduwar cutar da ya kaiga har kasafin kudin 2020 sai da aka zaftare shi domin ayi gudanar da wasu ayyukan.

Share.

game da Author