Akalla Mahara 200 ne jiragen saman yakin Najeriya suka yi ragaraga a dazukan Jibia dake jihar Katsina da Kurmi, jihar Zamfara.
Kodinaton yada Labarai na sojojin Najeriya, John Enenche ya ce an yi wa wani maboyar mahara daka Ibrahim Mai a Jibiya luguden wuta ta sama kuma sun kashe mahara da dama. Eneche ya ce Sojoji sun samu labarin cewa a wannan wuri be ake jibge shanun da aka sace wa fulani kuma maboyar gaggan masu garkuwa da mahara.
Bayan haka sojojin saman sun ragargaji Wasu maharan a Kurmi, karamar Hukumar Zurmi, jihar Zamfara.
Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya ya nuna farin cikin sa matuka bisa wannan nasara da dakarun sa suka samu yana mai cewa za a tura wasu jiragen zuwa yankin Kaduna, Neja da Kogi domin fatattakar iren-iren wadannan bata gari.
Discussion about this post