KORONA: Mutum 313 sun kamu, saura kiris Najeriya ta kai mutum 8000

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 313 da suka kamu da Korona a Najeriya ranar Lahadi.

Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Lahadi ya nuna Jihar Legas ta samu karin mutum 148, 36-FCT, 27-Rivers, 19 Edo, 13-Kano, 12-Ogun, 11-Ebonyi, 8-Nasarawa, 8-Delta, 7-Oyo, 6- Plateau, 5-Kaduna,4-Kwara,3-Akwa Ibom, 3-Bayelsa, 2-Niger
1-Anambra.

Yanzu mutum 7839 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 2263 sun warke, 226 sun rasu.

Idan ba a manta ba a makin da jiya, Shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa akwai yiwuwar za a fara sallaman wadanda suka kamu da Korona da suka fara jin sauki daga asibitocin kasar nan.

Ihekweazu ya fadi haka ne a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 a Abuja.

Ya ce gwamnati na yunkurin daukan wannan mataki ne bisa ga sakamakon binciken da aka gabatar game da cutar dake nuna cewa za a iya sallaman wanda ke dauke da cutar daga asibiti idan ya fara jin sauki a jikinsa. Zai koma gida ya killace kan sa ma’aikata na zuwa suna duba shi suna bashi magani.

” Muna duba yiwuwar wannan abu har yanzu domin ganin ko za a yi aiki da shirin a kasar nan. Sannan muna wayar wa mutane kai game da haka saboda gujewa korafe-korafen da za su yi idan gwamnati ta amince a rika haka.

Share.

game da Author