‘Yan Najeriya sun kashe naira Tiriliyan 22.8 akan abinci a shekarar 2019, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta kasa ta fitar.
Hakan ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun kashe kusan kashi 57% na kudaden su a akan abinci a shekarar 2019.
‘Yan Najeriya sun kashe akalla naira Tiriliya 4 a abincin gidajen abinci, mashaya, wuraren saida tuwo da danwake da amala, kamar yadda rahotan NBS na watan Mayun 2020 ya nuna.
Sannan kuma ‘yan Najeriya sun kashe naira Tiriliyan 2.5 wajen siyan abinci kamar su doya, dankali, falanten da sauran su. An ci shinkafar naira tiriliyan 1.9 sannan kuma da ganyayyaki na naira tiriliyan 1.7 duk a shekarar 2019.
Abubuwan da ba a kashe musu kudi sosai ba sun hada da kayan shaye-shaye da a aka kashe musu naira biyan 296.6, sai kuma bredi, chinchin da sauran kayan filawa da ‘yan Najeriya suka naira biliyan 205.5, sannan kuma sun kwankwadi Lemo da barasa har na naira biliyan 150.2.
Wannan rahoto ya nuna cewa yan Najeriya sun kashe akalla naira Tiriliyan 17.4 a abubuwan da ba na ci bane, wato ba abinci ba.
A harkar sufuri kuwa, ‘yan Najeriya sun kashe naira Tiriliyan 2.6 a wajen tafiye-tafiye, zuwa asibiti da kudin magani kuma sun kashe naira naira tiriliyan 2.6, biyan kudin makaranta kuma sun kashe naira Tiriliyan 2.4 sai kuma harkar waya da ‘yan Najeriya suka kashe naira tiriliyan 2.2.
‘Yan Najeriya sun biya kudin hayan naira Tiriliyan 2.1, man fetur da wutan lantarki kuma sun kashe naira Tiriliyan 2, kayan sakawa kuma da takalma, an yan najeriya sun kashe naira Tiriliyan 1.8, kayan aikace-aikacen gida kuma naira Tiriliyan 1.1, shakatawa da nishadi kuma sun kashe naira biliyan 428.2 sai kuma ruwan sha, naira biliyan 197.6.
Mutanen yankin Kudu maso Yamma (South-West) sun fi kashe kudi a shekarar 2019 dake da kashe 29.95%. Sai kuma Kudu Maso Kudu dake da kashi 20.94%, sai yankin Arewa maso Yamma, 17.02%.
Mutanen Jihar Legas sun fi kashe kudi fiye da kowacce jiha a shekarar 2019, domin an kashe akalla naira Tiriliyan 5.1, sai jihar Oyo da mutanen cikinta suka kashe naira Tiriliyan 2.3, sai jihar Delta naira tiriliyan 2.1 sai jihar Ribas, naira Tiriliyan 2 a karshe sai jihar Kano da aka kashe naira Tiriliyan 1.97.
Jihohin Yobe Naira biliyan 420, Nasarawa Naira biliyan 383.6 , Ebonyi, naira biliyan 310.2 da Taraba, Naira 297.4 ne aka samu mafi karancin hada-hada da kudi a shekarar 2019.