Kakakin Asibitin gwamnatin tarayya dake jihar Ogun, Segun Orisajo ya bayyana cewa wani jami’in dan sanda ya rasu a asibitin a dalilin kamuwa da cutar Coronavirus.
Orisajo ya ce an kawo wannan dan sanda asibitin ba shi da lafiya. Bayan an kwantar dashi sai aka dibi jinin sa domin y masa gwajin Coronavirus.
Sai dai ko da aka dawo da sakamakon gwajin da ya nuna ya kamu da cutar, dan sandan ya rasu. Kwanan shi uku a akwanci kafin ya cika.
Zuwa yanzu mutum 115 ne suka kamu da cutar Coronavirus a jihar Ogun.
Idan ba a manta ba a ranar Asabar, Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya nuna takaicin sa da rashin jin dadi kan yadda mutanen jihar ke karya dokar Coronavirus bayab an bude gari.
Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa gwamnati za ta garkame jihar, ba shiga, ba fita idan mutane suka ci gaba da bijire wa dokar kiyaye wa daga kamuwa da cutar coronavirus.
Sanwo-Olu ya ce yadda mutane suke cakuduwa a kasuwanni da bankuna ya bani takaici domin. Sam mutane basu kiyaye ba ko kadan kuma ba za mu bari a cu gaba da haka ba.
” Idan mutane suka ci gaba da yi wa doka taurin kai, toh gwamnati za ta garkame jihar, kowa ya koma gida ya ci gaba da zama har sai an iya shawo kan yaduwar cutar a jihar.