KIDIDDIGA: Yadda ‘yan Legas suka nunka Kanawa yin hidima da kudade a 2019

0

Hukumar Kididdiga ta Kasa ta bayyana cewa an sayi abinci na naira tiriliyan 22.8 cikin 2019. Wannan adadin jimillar kudade sun nuna cewa an kashe kashi 57 na jimillar kudaden da ‘yan Najeriya suka kashe cikin 2019.

Rahoton wanda aka fitar cikin watan Mayu din nan, ya ce ‘yan Najeriya sun kashe zunzurutun kudi har naira tiriliyan 40.2 cikin 2019.

“An ci abincin naira tiriliyan 4 godajen cin abinci, mashaya, gefen titi da wuraren shakatawa har na naira tiriliyan 4 a cikin 2019. Wadannan ciniki ne na abincin da aka ci a waje, ba wanda aka dafa a gida ba.”

Doya, Dankali: Rahoton ya ce an ci kayayyakin abinci irin su doya da dankali da makamantan su har na naira tiriliyan 2.5.

Shinkafa: Har ila yau, rahoton ya nuna a cikin 2019 an ci shinkafa ta naira tiriliyan 1.9. Amma bai tantance yawan shinkafar gida da ta waje da aka ci ba.

Kayan Miya: Rahoton ya yi kididdigar cewa an sayi kayan miya na kimanin naira tiriliyan 1.7.

Kayan da ba abinci ba:

1: An kashe naira tiriliyan 2.6 wajen zirga-zirga da sufuri.

2. ‘Yan Najeriya sun kashe naira tiriliyan 2.5 wajen kula da lafiyar kan su.

3. ‘Yan Najeriya sun kashe naira tiriliyan 2.4 wajen kula da ilmin kan su da na ‘ya’yan su a cikin 2019.

4. Tarho na wayar selula ya kwashe naira tiriliyan 2.2 na kudin da ‘yan Najeriya suka kashe cikin 2019.

Gidajen Haya:

Yan Najeriya sun biya haya ta zunzurutun naira tiriliyan 2.

Fetur Da Gas:

‘Yan Najeriya sun sha fetur da gas na naira tiriliyan 2.

Kayan Amfani A Gida: ‘Yan Najeriya su kashe har naira tiriliyan 1.1 wajen sayen kayan da suke amfanin yau da kullum da su a gida.

Shakatawa: ‘Yan Najeriya sun kashe naira bilyan 428.2 wajen shakatawa da suka hada da kallon finafinai a sinimomi da sauran harkokin da suka danganci haka.

Lemuka Da Jus: ‘Yan Najeriya sun kwankwadi lemuka, madara da jus har na naira bilyan 296.6.

Biredi Da Cincin: ‘Yan Najeriya sun kashe naira bilyan 205.5 wajen ci biredi, cincin da duk wasu nau’o’in biredi.

Barasa: ‘Yan Najeriya sun yi mankas da barasa har ta naira bilyan 150.2 a cikin 2019.

Yankin Da Ya Fi Kashe Kudi: Shiyyar Kudu maso Yamma ce ta ci kashe kudi cikin 2019. Ta kashe kashi 29.95 na yawan kudaden da ‘yan Najeriya suka kashe cikin 2019. Kudu maso Kudu sun kashe kashi 20.94, Arewa maso Yamma kuwa ta kashe kashi 17.02.

Jihar Da Ta Fi Kashe Kudi: ‘Yan Jihar Legas sun kashe naira tiriliyan 5.1 cikin 2019, Oyo naira tiriliyan 2.3, Delta naira tiriliyan 2.1, Rivers naira tiriliyan 2, Kano naira tiriliyan 2 ita ma.

‘Yan jihar Taraba ne kutal, na karshe a kashe kudade cikin 2019. Sun kashe naira bilyan 297.4 kacal.

Share.

game da Author