Tun kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya kara masa karfin-fada-a-ji a zangon sa ba biyu, tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Abba ya ja zaren sa iyakar karfin sa tun a cikin shekaru hudu na farkon mulkin Shugaba Buhari.
Tun kuma kafin rasuwar sa a ranar Juma’a, an sha fada tun tuni cewa karfin sa ya wuce makadi-da-rawa a fadar shugaban kasa. Ko da yake da dama ana ganin cewa shi fa Kyari aikin da aka sa shi ne ya ke yi, don haka duk abin da ya yi, to cikin aikin sa ne kawai.
Ya zama Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa a cikin Augusta, 2015. Tun daga lokacin ne kuma aka rika yi masa kallon shi da irin su dan’uwan Buhari, wato Mamman Daura, su ne ‘yan fadar shugaban kasa, sai abin da su ke so Buhari ke yi.
Shi da kan sa Kyari, ya sha daukar alhakin wata gazawa da Buhari ya yi, ya dora laifin a kan sa.
ABBA KYARI DA AISHA BUHARI:
Tun tafiyar mulki ba ta yi ni sa ba sosai a zango na farko, uwargidan Buhari, Aisha, ta fito kakara ta yi korafin cewa wasu ‘yan kalilan din ‘yan-ba-ni-na-iya ne ke rike da gwamnati, ba mijin ta Buhari ba.
Sai da ta kai Aisha ta fito ta ambaci Abba Kyari, har ta kara da cewa idan haka gwamnatin za ta ci gaba, to ba za a yi kamfen na 2019 tare da ita ba.
ABBA KYARI A MA’AUNIN EL-RUFAI:
Cikin 2016 an fallasa wata wasika da Gwamna Nasiru El-Rufai ya rubuta wa Shugaba Buhari a asirce, inda ya yi raga-raga da irin yadda Abba Kyari da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ke katsalandan a cikin sha’anin jam’iyyar APC da wasu al’amurran da ce Kyari na yi wa shiga-sharo-ba-shanu.
“Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa bai san komai ba a sha’anin jam’iyyar APC. Ba da shi aka kafa jam’iyyar ba, ba da shi aka yi zaben fitar-da-gwani ba, kuma ba da shi aka yi kamfen ba….”
El-Rufai ya ce ba da Kyari aka sha wahalar komai ba a APC. A siyassr ma shi sabon-yanka-rake ne.
ABBA KYARI DA HARKALLAR MTN:
An zargi Kyari da karbar toshiyar-baki ta zunzurutun kudi naira milyan 500 daga kamfanin MTN, domin ya sa baki a rage wa kamfanin diyyar makudan kudaden da Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta kakaba masa.
An dora wa MTN tarar dala bilyan 5 saboda karyar dokar Najeriya. Abba dai ya karyata zargin da aka yi masa. Shi ma MTN ya ce bai bayar da toshiyar bakin adadin kudaden ba.
ABBA KYARI DA BABAGANA MONGUNO:
Wata kwatagwangwama, karimtsa da rimatson riciki da Kyari ya tsoma kan sa, ya fito fili daga wasikun da Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, Abba Kyari, ya rubuta wa Shugabannin Fannonin Tsaro, inda ya gargade su da su daina karbar umarni daga Abba Kyari.
Babagana Monguno ya zargi Kyari da yin kane-kane a sha’anin tsaron Najeriya, har ta kai ya kan kira su Janar Buratai taro, ba tare da sanin Monguno ba.
Ya ce bai ga dalilin da Kyari zai rika yin katsalandan a sha’anin kasar nan ba, tun da ba shi da hurumin yin hakan.
ABBA KYARI DA IBE KACHIKWU:
Cikin 2017, tsohon Karamin Ministan Harkokin Mai, Ibe Kachikwu, ya yi korafin cewa sau da dama idan ya na so ya gana da Ministan Man Fetur, wato Shugaba Buhari, amma Kyari sai ya hana shi.
Tuwo-Na-Mai-Na
Sunan Kyari ya kara shiga cikin sabarkala, yayin da aka dana ‘yar sa babban mukami a asirce, Najeriya ba su sani ba.
An nada ‘yar sa Mataimakiyar Shugabar Hukumar NSIA, ba tare da an buga tandar neman duk wanda ya cancanta ya fito ya nemi aikin ba.
ABBA KYARI DA YEMI OSINBAJO
Abba Kyari ya yi wa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo kafar-ungulu, inda ya sa Buhari ya kwace aikin sasanta rikicin Fulani da Makiyaya daga Ofishin Osinbajo, ya maida ofishin Kyari.
Sannan kuma ya yi sanadiyyar rushe Kwamitin Osinbajo Tallalin Arziki (EMT), aka maye gurbin sa da Majalisar Shawarar Harkokin Tattalin Arziki (EAC).
ABBA KYARI NE TSANIN GANI NA -Buhari
Duk da wannan cukumurdar karambosuwar kutunguilar mulki da aka rika tabkawa, Buhari ya kara wa Kyari matsayi, inda bayan sake rantsar da shi a karo na biyu, ya shaida wa Ministocin da ya nada cewa, “duk mai son gani na, ko mai wata wasika zuwa gare, sai ya biyo ta hannun Abba Kyari tukunna.”