YIN MURNAR RASUWAR ABBA KYARI: Ganduje ya fatattaki Kwamishinan Ayyukan jihar, Magaji Mu’azu

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya fatattaki kwamishinan Ayyukan jihar, Engr. Mu’azu Magaji daga kujerar kwamishina a jihar.

hakan ya biyan kalaman batanci da ya rika yi bayan samun labarin rasuwar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Abba Kyari.

Kwamishinan Yada labarai, Muhammad Garba ya fitar da wannan sanarwa, yana mai cewa gwamna Ganduje ya fusata bisa yadda kwamishina Mu’azu ya rika nuna farincika da kalamai da basu dace ba ga mamacin.

Ganduje ya ce bai kamata ace ma’aikacin gwamnati ya rika yin irin haka ba, ganin cewa zai iya sa aga kamar matsayin gwamnatin jihar kenan kan marigayi Abba Kyari.

A karshe gwamna ganduje yayi fatan Allah ya ji kansa ya sa ya huta.

Marigayi Abba Kyari ya rasu ranar, juma’a a wani asibiti dake Legas. An yi jana’izar sa a Abuja ranar Asabar.

Share.

game da Author