Ainihin shekarun Marigayi Abba Kyari

0

PREMIUM TIMES ta yiwo bincike mai zurfin domin gano ainihin ranar haihuwar marigayi Abba Kyari.

Babban dalilin haka kuwa shine, ganin yadda kafafen yada labarai ke ta kintata shekarun a rashin sanin ainihin ranar haihuwar Marigayi Kyari.

Sanin kowa ne cewa marigayi Kyari shine hadimin Buhari da ya fi karfi da karfin iko acikin wadanda ke yi wa shugaba Buhari aiki.

A 2019, Buhari ya fito karara inda ya bayyana cewa sai Abba Kyari yayi maka iso kafin ka iya ganin sa ko kuma ma ya saurare ka.

PREMIUM TIMES tabi diddigin takardun karatun Abba Kyari da na aikin da kuma yin bincike mai zurfi domin gano ko yaushe ne aka haifi marigayi Abba Kyari.

Ya tabbata an haifi Marigayi Kyari ranar Talata 23 ga watan Satumba, 1952 da ya nuna cewa ya rasu yana da shekara 67 kenan.

Wani abu da ba a taba fadi ba shine, babu wani lokaci da aka taba bayyana shekarunsa kai tsaye daga mahukunta ko a lokacin da aka nada shi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Wasu jaridun sukan saka shekarun sa ya zarce 81, wasu sama da 70.

Allah yayi wa Marigayi Abba Kyari, rasuwa ranar Juma’a a wani Asibiti a Legas. An yi jana’izan sa ranar Asabar a Abuja, inda babban malami, kuma ministan sadarwa, Ali Pantami ya jagoranta.

Allah ya ji kansa, Amin.

Share.

game da Author