Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, mai kowa, mai komai, mai bayar da mulki ga wanda yaso. Mai kashe wa, mai raya wa, mamallakin kowa da komai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaban mu, Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.
Ya Mai girma shugaban kasa! Ya masu daraja manyan arewa!! Ya dattawan arewa!!!
Alhamdulillah, kwanakin baya, har mun fara murna da jin dadi da farin ciki cewa, fadar shugaban kasa ta sa baki cikin rikicin masarautar Kano da gwamnati, har muna ganin cewa da ikon Allah wannan matsala ta zo karshe ke nan. Muna cewa duk wani tsoron da muke ji na faruwar tashin hankali da zubar da jinin bayin Allah da bata dukiyoyin su zai gushe da karfin ikon Allah, kuma Allah ba zai bari ya faru ba. Idan za ku iya tunawa, a can kwanakin baya, mun samu labari cewa fadar mai girma Shugaban kasa ta kafa kwamitin sasanta rikici tsakanin gwamnatin Kano da masarautar Kano, karkashin jagorancin mai girma, mai daraja, tsohon shugaban kasar Najeriya, Janaral Abdus-Salami Abubakar. Sannan da kuma kokari da yunkurin da muka samu labari cewa, manyan mu, dattawan arewa, masu daraja, karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi suna yi, domin dai duk a kawo karshen wannan rigima da badakala da ke faruwa. Da dukkanin kokarin da wasu daga cikin malaman mu suke yi, domin dai duk kokarin kaucewa tashin hankali da rigima, da kokarin su na ganin an zauna lafiya; to ashe-ashe duk wannan bai sa gwamna Ganduje ya yarda a zauna lafiya tsakanin sa da Mai Martaba Sarki ba.
Sai ma yanzu muka samu labari daga majiya mai tushe kuma kwakkwara, wadda babu wasa a cikin ta, cewa gwamnan ya sake bullo da wata hanya ta wulakanta masarautar Kano da kara zubar mata da mutunci.
A inda ya kira kakakin majalisa da ‘yan majalisu, ya gana da su cikin sirri, yayi masu alkawarin kudi masu tsoka, domin wai su taimaka su tsige masa Mai Martaba Sarkin Kano. Kuma duk wannan, ba tare da wani dalili ko wata kwakkwarar hujja ba da za’a nuna ace Sarkin yayi. A baya ma kafin gwamnan yaci zabe, mun samu labari cewa ya bai wa wasu daga cikin hakimai kudi, wai don su mara masa baya ya cire Sarkin Kano.

Ya ku jama’ah, a halin da muke ciki dai yanzu, mutane da dama da suka sa baki cikin lamarin sulhu, tuni suka fahimci cewa shi dai gwamna Ganduje ba ya kaunar Sarkin ne kawai, kuma sam baya kaunar zaman lafiyar al’ummar jihar Kano da ma arewa baki daya. Domin kuwa babu wani kwakkwaran dalili na wani laifi da za’a nuna ace Sarkin yayi masa, illa kawai zarge-zargen cewa wai ya marawa wata jam’iyyar siyasa baya a lokacin zabe, wanda wannan zargi ne kawai da baya da tushe bare makama!
Ya mai girma shugaban kasa! Ya ku manyan arewa!! Ya ku dattawan arewa!!! Idan aka yi la’akari da yadda jihar Kano ta kasance babbar jiha a tsakiyar yankin arewa, jihar da Allah ya kare, take zaune lafiya babu wani tashin hankali, babu tarzoma, shi yasa nike jawo hankalin ku, nike yi maku nasiha, a matsayin ku na manya na, shugabanni na, iyaye na, cewa, lallai ya zama wajibi a kiyaye da al’amuran da zasu kawo tashe-tashen hankula da zubar da jini, da asarar dukiyoyi. Musamman la’akari da yadda matasan jihar Kano, da al’ummar Kano suke yin cin-ci-rin-do, kwararo-kwararo, lungu-lungu, sako-sako, suna daga hannuwa, suna yin jinjina ga Sarkin su, tare da nuna goyon bayan su, da kaunar su, da soyayyar su a gare shi.
Lallai wannan abin kiyaye wa ne, domin kar a tsokano wa Kanawa da arewa baki daya rigimar da ba zata haifi da mai ido ba. Da ma dai kowa yasan irin halin da arewa ta ke ciki yanzu na rashin tsaro. To wallahi, mu nemi hanyar da Allah zai magance muna shi, ba wai kuma wasu ‘yan siyasar mu su rinka tsokano wasu rigingimun ba!
A labarin da ke iske mu yau, kuma wallahi labari ne mai tushe, kun san ba zamu yi karya da sharri ko kazafi akan kowa ba, domin lahirar mu muke kallo ba duniya ba. Mun san za mu mutu, mu tashi a gaban Allah mahaliccin mu. Daga cikin makircin da aka kulla, wai a cire Mai Martaba Sarkin Kano, an rubuta fetishan guda biyu, an aika zuwa ga majalisar wakilan jihar Kano. Wai ‘yan majalisa za su yi bincike akan Sarkin, sannan su tabbatar wa da gwamna cewa a cire Sarkin. Wannan shine yarjejeniyar da aka kulla, tsakanin gwamna da ‘yan majalisar kwana biyu da suka wuce.
Sannan na biyu, an shirya cewa, hukumar yakar cin hanci da rashawa za ta gayyaci Mai Martaba Sarki, domin wai yazo ya kare kan sa daga tuhume-tuhumen da ake yi wa masarauta. Wannan ina son ku fahimci cewa, wani tarko ne aka dana wa Mai Martaba Sarki. Domin idan yazo kare kan sa a gaban wannan hukuma, shirin shine, za’a dakatar da shi, da sunan cewa wai Sarki ya zubar da mutuncin masarauta. Idan kuwa yaki zuwa, sai su dakatar da shi, cewa wai ya nuna taurin kai ga hukuma. Wannan shine sharri, da gadar zaren da suka kulla wa Mai Martaba Sarkin Kano, wanda da ikon Allah, munyi imani, tun da Allah ba ya zalunci, kuma baya son azzalumai, duk wannan sharri, Sarki zai tsallake shi da karfin Mai duka (Allah).
Saboda haka, ya kamata shugaban kasa yasan wannan, manyan mu su san wannan, ‘yan arewa su san wannan, dukkanin ‘yan Najeriya su san wannan! Domin kar wani abu ya faru (Allah ya kiyaye) ace ba mu fada ba. Mun fada, mun fada, mun fada, kuma duk duniya ta shaida. Duk wani mai hakki mun ba shi hakkin sa. Saboda haka har ga Allah mun fita.
Shin shugaban kasa da manyan mu na arewa sun san irin yadda muka zama abun dariya a wurin abokan zaman mu na kudu kuwa, akan wannan matsala? Suna ganin cewa yaya za’a yi, wannan ‘yar rigima, ace an kasa shawo kan ta?
Don Allah, don Allah, don Allah ina roko ya kamata wannan al’amari ya tsaya haka nan!
Sannan shi kuma gwamna Ganduje, da dukkanin mukarraban sa, da dukkanin masu goyon bayan wannan raba kan al’ummmah da yake yi, ya sani, wallahi wata rana ba shine gwamnan jihar Kano ba. Wasu sun yi kafin shi, sun wuce, kuma daga su sai aikin da suka shuka, na alkhairi ko sharri. Kuma gwamna ya sani, Allah ba zai taba raga wa masu rarraba kan jama’ah ba. Ina rokon Allah ya shiryar da shi, ya ganar da shi gaskiya, ya bashi ikon bin ta, kuma ya ganar da shi karya, ya ba shi ikon guje mata, amin.
Ya Allah, muna tawassali da sunayen ka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka, ka kawo muna karshen zubar da jinin bayin Allah da ke faruwa a yankin mu na arewa.
Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah, Muhammad (SAW).
Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, ya taimaki shugabanin mu da yankin mu na arewa, da Najeriya baki daya, amin.
Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun! Allahu Akbar!!
‘Yan uwa ina mai sanar da ku cewa an sake yin wani rashin a gidan Dabo. Na samu labari Nanin kofar Nasarawa daya daga cikin manyan ‘ya ‘yan Sarkin Kano, Khalifah Muhammadu Sanusi I, ta rasu a daren jiya talata, 03/03/2020.
Allahu Akbar!!! An yi rashin hamshakiyar basarakiya, mutuniyar kirki, mai zumunci, mai hakuri.
Ina mika sakon ta’aziyyah ta zuwa ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, da dukkanin bani Dabo. Allah ya jikan ta, ya gafarta mata, yasa Aljannah Firdawsi ta zam makomarta, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.