RIKICIN APC: Oshiomhole ya daukaka kara

0

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole da Babbar Kotun Abuja ta dakatar a ranar Laraba, ya daukaka. Sai dai duk ya daukaka karar, ba a sa ranar da za a fara karar ta sa ba.

Ya kai karar ce ya na neman a soke dakatar da shi da aka yi, da kuma hana shi shiga harabar Sakateriyar APC ta kasa da Mai Shari’a Danlami Senchi ya yi a Abuja.

Wani dan jama’iyyar APC mai suna Oluwale Afolabi ne yam aka Oshiomhole kara kotu, tun a cikin watan Janairu, inda ya nemi kotu ta hana shi kiran kan sa shugaban jam’iyyar APC na kasa, domin rashen APC na jihar Edo ya dakatar da shi daga mamba na jam’iyyar.

An dakatar da Oshiomhole ne a daidai lokacin da ya ce ruguntsimin rikici da Gwamnan Jihar Edo wanda ya gaje shi, Godwin Obaseki.

Obaseki da Mataimakin sa su na kakudubar rikici da Oshiomhole, saboda a cewar su, shugaban na APC na Kasa ya na so ne ya jefa kowa a cikin aljihun sa a jihar Edo, sai abin da ya ga damar yi da su, kuma sai abin da ya ce ya ke so kowa ya rika yi a jihar, ciki har da gwamnan kan sa da mataimakin sa.

Obaseki y ace Oshiomhole na so ya dawo da siyasar ubangida a Jihar Kogi, bayan kuma shi da Oshiomhole sun ki yarda a gina siyasar ubangida a jihar, a lokacin da shi Oshiomhole ke gwamna tsawon shekaru takwas a jihar.

Sannan kuma wasu shugabannin APC na zargin Oshiomhole da rura wutar rikicin jam’iyya a waso jihohi, abin da ya haddasa jam’iyyar ta rasa jihohi kamar Rivers, Bayelsa, Zamfara, Adamawa da Oyo.

A cikin takardun daukaka karar da Oshiomhole ya yi a ranar Alhamis, wadanda suka fado hannun PREMIUM TIMES, ya kalubalaci dakatar da shi da kotu ta yi.

Cikin wadanda Oshiomhole ya hada ya kai kara har da Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Shiyyar Arewa maso Gabas, Salihu Mustapha.

Akwai kuma Shugaban Jam’iyyar APC Reshen Jihar Edo, Anselm Ojezua, wanda dan gaban-goshin Gwamna Obaseki ne mai fada da shi Oshiomhole din.

Sauran sun hada da Sani Gomna, Oshawo Steven, Fani Wabulari, Princewill Ejogbarado, Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya da kuma Hukumar Tsaro ta SSS.

Ba a dai sa ranar da kotu za ta fara sauraren wannan kara da Oshiomhole ya daukaka ba.

Share.

game da Author