Rashin nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Livepool ta yi sau uku a jere, ya bai wa kusan kowa mamaki a duniyar kwallon kafa.
Kafin nan kuwa, kungiyar ta yi rashin nasara ce sau daya tal tun da aka fara wasan Premier na shekarar 2019/2020.
Sai dai abin mamaki, a daidai lokacin da ake ganin wasanni hudu kacal suka rage wa kungiyar ta dauki kofin Premier, sai ta hadu da rashin nasara a wasanni uku da gasanni uku da ke ciki.
Yayin da Atletico Madrid ta ci Liverpool 1:0 a gasar Champion’s Legue, sai ita kuwa Watford ta karya mata kwari, inda a gasar Premier ta sharara mata wallaye 3:0.
Talata kuma da dare a wasan kusa da na karshe, Chelsea ta yi nasara a kan Liverpool da ci 2:0.
Mugun Bakin Daragh Curley Kan Liverpool
Cikin watan Janairu kusa da karshen sa, wani yaro dan shekara 10, mai suna Daragh Curley, wanda masoyin kungiyar Manchester United ne, ya rubuta wa kociyan Liverpool wasika, ya aika ta Gidan Waya, kuma wasikar ta samu Jurgen Klopp har gida.
Daragh, wanda ke karatu a karamar makarantar garin Donegal, shi da mahaifiyar sa sun cika da mamakin yadda Klopp ya samu lokacin da ya maida wa yaron amsa main dauke da dogon rubutu.
Mahaifiyar sa mai suna Tricia ta je Gidan Wayar McFaddens a Glenswilly, sai jami’an wurin suka ce mata ai kuwa akwai wata wasikar musamman da aka aiko mata. Don haka bari a dauko mata.
Yayin da ta kai wa Daragh ya bude wasika, sai ya ga ashe Klopp ne da kan sa ya maida masa doguwar amsa.
Abin Da Wasikar Daragh Ta Kunsa
Daragh wanda ke karatu Glenswilly National School, ya yi wa Klopp wasika mai dauke da roko da kuma fatan su rage cin kwallaye, ko kuma su rage yin nasara a kan sauran kulob-kulob haka nan.
Ya Rubuta: “Liverpool din nan sai cin kwallaye kawai ta ke yi, ta na nasara a wasanni da yawa. Gaskiya kwata-kwata rai na ya na baci, a matsayi na mai goyon bayan Manchester United.
“Ina fatan idan Liverpool ta sake buga wasa gaba, zan so ta yi rashin nasara, (Domin ita ma ta ji irin haushin da mu ke yi).
“Ai gar aka bar sauran kulob su ma su ci kwallaye haka nan. Ina fatan za ka gamsu da fatan da na ke yi, kada ka ci kofin Premier League da ma duk wani kofi a wannan kakar wasan.”
Amsar Wasika Daga Kociya Klopp
Klopp ya rubuta masa cewa, “Na fahimci wasikar ka. Duk da dai ba ka taya mu murna ko fatan allheri ba, to na ji dadi, kuma na yi murna da samun wasikar ka. Dama ni mutum ne mai son jin ta bakin kananan yara masu sha’awar kallon kwallon kafa.
“Amma dai a wannan roko da ka yi min wai na sa kungiya ta ta yi rashin nasara, ba zan amince da kai ba.
“Aiki na ne na ga Liverpool na yin nasara, saboda a duniya akwai milyoyin mutanen da ke son ganin hakan ya tabbata. Don haka ba zan iya bada musu kasa ko toka a ido ba. Ba zan so su ki yin nasara ba.
“Sai ka yi murna, domin ai can a baya mun taba yin rashin nasara. Kuma nan gaba ma za mu sake yin rashin nasarar.”
“A karshe, ina alfahari da kai, kamar yadda ka ke alfahari da Manchester United din ka. Ita ma United din ta yi sa’a da ta samu yaro mai kishin ta kamar ka.”
Tun bayan wasikar da yaron ya aika wa Klopp dai an ci Liverpool har sau uku a jere.
Shi kan sa mahaifin yaron, mai suna Gordon Curley, wanda shi ma mai goyon bayan Manchester United ne, sai da amsar da Klopp ya maida wa dan sa ta ba shi mamaki.
Kuma ya ce dama shi Klopp ya na burge shi matuka.
Daragh dai ya cika da murna da mamakin amsar da Klopp ya rubuto masa, har ma washegari ya dauki wasikar ya kai makaranta, ya rika nunawa ‘yan ajin su.
Wadannan wasiku biyu dai kusan dukkan jaridu da mujallun Ingila sun buga su.
Sannan kuma Manchester United ta aika wa yaro da mahaifin sa takardar gayyata ta musamman domin halartar kallon wasan kungiyar.
Tambayar da masu sharhi key i a nan, shin ko Liverpool za ta bari a sake yin nasara a kan ta?
Sai mu je Ingila mu tambayi karamin yaro Dagagh.
Discussion about this post