Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa za ta gabatar da muradin ta na neman yi wa dokokin zabe 34 kwaskwarima, wadanda ke cikin Kundin Dokokin Zaben 2010.
Daga cikin kwaskwarimar da ta ke so a yi a cikin dokokin, har da samar da hukunce-hukunce da ladabtarwar da za a yi wa duk wani wanda ya karya dokar zabe kafin, bayan ko kuma a lokacin da ake gudanar da zabe.
Hukumar ta kara da cewa kudirin da ta ke son gabatarwa kuma zai samar da hurumin dokar tsaro sosai, wadda za ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a a lokacin zabe.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a taron bibiyar tsare-tsaren dokokin da suka jibinci harkokin zabe, wanda ya gudana a Lagos.Taron na hadin guiwa ne tsakanin INEC, Cibiyar Goyon Bayan Zabukan Dimokradiyya ta Turai (ECES) da kuma Gidauniyar Tallafa Wa Zabuka ta Kasa-da-kasa (IFES).
Yakubu ya ce tun kafin zaben 2019 INEC ta karbi tubutaccen kudirin daga Kwamitin Kula Da Zabe na Majalisar Dattawa, kuma suka mika shi ga gwamnati domin amincewa a sa masa hannu ya zama doka.
Ya ce tuni INEC ta raba kwafe-kwafen kudirin sabbin dokokin da za a yi wa kwaskwarimar ga Kwamishinonin Zabe na Kasa, Daraktocin Zabe na Kasa da sauran manyan jami’an zabe a jihohi 36 na fadin kasar nan.
Sai An Rika Hukunta Masu Karya Dokokin Zabe Sannan A Magance Matsalolin Zabe.
Shugaban INEC ya ce, “matsawar dai ba a hukunta masu karya dokokin zabe yadda suka ga dama, to za a dade ana ci gaba da samun matsaloli a tafiyar zabuka a kasar nan.
“Shi ya sa mu ke so a yi wa wasu dokokin kwaskwarima, ta yadda tilas duk wanda ya karya dokar zabe sai an hukunta shi.
“Duk kasar da ba ta hukunta masu karya dokar zabe, to ta shiga uku, Don haka tilas sai an samar da hurumin dokokin da za su rika hukunta masu karya dokar zabe, domin ta haka ne kawai za a iya dakile rashin mutuncin da wasu ke yi a lokacin zabe, idan ma har ba a magance shi kwata-kwata ba.”
Yakubu ya ce yi wa dokokin zabe kwaskwarima zai kuma bai wa mutane masu nakasa damar yin zabe, sannan su ma mata za su kara samun gurabu a zabukan kasar nan a karkashin dokokin da za a yi wa kwaskwarima.