KAKUDUBA A APC: Mataimakin Oshiomhole ya zarge shi da take umarnin kotu na dakatar da shi

0

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa na Shiyyar Arewa maso Gabas, Salihu Mustapha, ya zargi Shugaban Jam’iyyar na Kasa da kotu ta dakatar, cewa ya na kokari ya take umarnin kotu.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wadda ke karkashin Mai Shari’a Danlami Senchi ce ta dakatar da Adams Oshimhole daga shugabancin APC.

Ta dakatar da shi ne bayan an kai mata korafin cewa tunda an dakatar da shi daga APC ta jihar Edo, bai kamata ba ya ci gaba da rikon jam’iyyar a matsayinnshugaban ta na kasa kuma.

Shi kuma Mataimakin Shugaba Salihu Mustapha, cewa yay i ai tunda anndakatar da Oshiomhole, to duk wani umarni ko aiki da ya yi ko zai yi da sunan shugaban APC, haramtacce ne.

A wata hira da Mustapha ya yi ta wayar tarho da ‘yan jarida, jim kadan bayan dakatar da Oshiomhole, ya zarge shi da take umarnin kotu, inda ya umarci Kakakin APC na Kasa, Lanre Issa-Onilu da ya bayyana Waziri Bulama a matsayin Sakataren APC na Kasa.

Mustapha dai na daya daga cikin Shugabannin Kwamitin Zartaswa na APC, wanda ke kalubalantar tsarin shugabancin Oshiomhole.

Wakilin mu ya ta taba ganin yadda su biyun suka rika yi wa juna hargowa a wurin taron manyan jam’iyya, har shi Mustapha ya fusata ya fice daga wurin taron.

“Jim kadan bayan kotu ta bayar da umarnin ta dakatar da Oshiomhole, sai ya umarci Lanre Issa-Onilu da ya sanar da cewa Bulama ne Sakataren APC na Kasa.

Ya yi karin bayaninn cewa an yi taro na baya inda aka kasa cimma nasarar wanda za a nada, kuma aka tsaya a haka din.

“Na tabbatar ku ‘yan jarida kun san ba a cimma amincewa da wanda za a nada din ba, tun bayan wanda ke kai, Maimala Buni ya sauka ya zama Gwamnan Yobe.
“Don haka Oshiomhole na so ya kara cukurkuda matsalar jam’iyyar domin ta kara dagulewa kawai.

Da yawan ma’aikatan ofishin APC na Kasa da Premium Times ta zanta da su, sun yi murna da dakatar da Oshiomhole, wanda suka ce dama an gaji da salon mulkin san a karfa-karfa da ni-kadai-na-iya.

Bayan Dakatarwa: Kotu Ta Hana Oshiomhole Shiga Sakateriyar APC

A ranar Laraba ce Kotu ta dakatar da Oshiomhole daga shugabancin APC, sannan kuma ta umarci kada jami’an tsaro su bar shi ya sake shiga Sakateriyar APC ta Kasa, har sai bayan an an kammala shari’a an ga abin da kotu ta yanke daga karshe.

Babbar Kotun Tarayya da ke Jabi, Abuja, ta umarci Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole ya daina kiran kan sa shugaban jam’iyyar, saboda ta dakatar da shi.

Sannan kuma kotu ta ce kada a bar Oshiomhole ya sake shiga sakateriyar jam’iyya ta kasa.

Mai Shari’a Danlami Senchi, ya bada umarnin dakatarwar bayan da ya saurari wani korafi da aka gabatar a kan Oshiomhole, cewa tunda an dakatar da shi a cikin APC a Jihar sa ta Edo, to babu wani dalilin da zai sa ya ci gaba da zama shugaban APC na Kasa kuma.

Wani mai suna Oluwale Afolabi ne ya shigar da karar a ranar Laraba. Ya hada da Oshiomhole da kuma jam’iyyar APC ita kan ta duk ya maka su kotu.

Afolabi dai ya shigar da wannan kara ce tun a ranar 16 Ga Janairu, inda ya ce an dakatar da Oshiomhole daga cikin jam’iyyar APC a jihar Edo, kuma har zuwa yau bai kalubalanci dakatarwar da aka yi masa a kotu ba.

Don haka mai kara ya ce tunda Oshiomhole bai yi tankiyar dakatar da shi ba ta hanyar kalubalanta a kotu, saboda haka bai cancanta ya ci gaba da zama shugaban jam’iyya na kasa ba.

Wani babban lauya mai suna Damian Dodo ne lauyan da Oshiomhole da APC suka dauka.

Mai Shari’a Senchi a ranar Laraba ya ce kuskure ne Oshiomhole ya rika kira kan sa shugaban APC, sannan ita APC din kuskure ne ta ci gaba da rike shi a matsayin shugaban ta na kasa, tunda a mazabar sa, wato jihar Edo an dakatar da shi.

“Daga yau kada ka kara kiran kan ka shugaban APC na kasa, kuma kada ka sake amsawa idan aka kira ka shugaban APC na kasa, har sai bayan abin da hukuncin kotu ya zartas.”

Mai Sahri’a ya kuma umarci APC ka ta sake ta kara kiran Oshiomhole da suna ko lakabin shugaban ta na kasa.

Sannan kuma kotu ta ce kada a bar Oshiomhole ya sake shiga sakateriyar jam’iyya ta kasa.

Share.

game da Author