Mahukuntan Sojojin Najeriya sun sallami kananan yara 223 da ke tsare a Kurkukun Maiduguri da wurin tsaron masu laifi da sojoji suka tanadar.
An sallame su bayan an tantance su daga zargin kusanci da kuma mu’amala ko kuma yi wa Boko Haram aiki.
Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ce ta bada wannan sanarwa.
An damka yaran ga Ma’aikatar Harkokin Mata Da Inganta Al’umma ta Jihar Barno, UNICEF da kuma Gwamnatin Jihar Barno a Maiduguri a ranar Talata da dare.
Cikinn wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na UNICEF a Jihar Barno, Samuel Kaalu ya fitar a ranar Laraba, ya ce kananan yaran duk za a shigar da su a cikin wasu tsare-tsare domin sake maida su a hannun iyayen su da zaran sun kammala.
Kaalu ya ce da dama daga cikin yaran an samu rahotannin bacewar su tun bayan shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata. Wdansun su ma tuni an dauka sun mutu.
Wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya bayyana sakin yaran a matsayin wani babban matakin inganta rayuwar kananan yaran da ke zaune a yankin da ake fama da tashe-tashen hankula.
“Wadannan kananan yara sun cancacnci samun kulawa tun su na kanana, yanzu kuma su na bukatar taimakon sake shiga rayuwar su bta farko, bayan da Boko Haram suka tarwatsa su suka canja musu rayuwa a karfin tsiya.”
Dukkan yara dai sun shiga halin kunci, wasu sun rasa rayukan su, wasu sun koma rayuwar sansanin gudun hijira, wasu sun rasa iyaye, wasu kuma Boko Haram sun sace su, sun maida su masu yi musu mugayen ayyukan ta’addanci ba da son ran su ba.
UNICEF ta ce Boko Haram sun arce da kananan yara da dama tun daga 2012, su na saka su ayyukan ta’addancin kai hare-haren kunar-bakin-wake, su na kama yara mata su na yi musu fyade kuma su na dirka wa wasu ciki, sannan sun haihu ba tare da kulawar asibiti ba.
Abin Da Ke Faruwa Ga Kananan Yara A Maiduguri Daga 2016 Zuwa Yau
UNICEF ta ce daga 2017 zuwa yau sojoji sun sallami kananan yaran da ke da alaka da masu ta’addanci har su 1,743. Daga cikin su 1,125 yara maza ne, sai kuma yara mata 618.
“Idan aka hada da wadanda aka saki tun a 2016, sun zama kenan an sallami yara kanana har 3,559. Dukkan su kuma sai da suka yi zaman Saisaita Tunani da Rayuwar su a Cibiyar Bulunkutu Rehabilitation Center da ke cikin Maiduguri. Kuma tuni sun koma a hannun iyayen su.
Wadanda ba su da iyaye kuma an damka su ga wadanda suka cancanci kulawa da su, tare da ci gaba da samun tallafi.”
Ya ce UNICEF za ta ci gaba da hada guiwa da Najeriya wajen ceto rayuwar kananan yaran da suka tsinci kan su sun a mu’amala da masu ta’addanci.
Akalla mutane 12,264 ciki har da kananan yara suka samu irin wannan kulawa tun daga 2017.
A cikin 2019, Hukumar Tsaro ta Sojoji ta damka kananan yara 86 da ke yi wa Boko Haram ayyukan kai hare-hare. Ta damka su ne ga Cibiyar Barno Rehabilitation Center da ke Bulunkutu. Haka Hedikwatar Tsaron Sojojin Najriya ta bayyana.