PDP za ta koma Kotun Koli domin jayayyar sake duba hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa

0

Jam’iyyar adawa PDP, ta zargi jam’iyya mai mulki APC laifin matsa lamba ga alkalan Kotun Koli don su warware hukunci zaben Zamfara da na Beyelsa.

PDP ta ce idan har APC za ta kalubalanci sakamakon zaben Bayelsa da na Zamfara, to ita ma PDP za ta koma Kotun Koli damin ta a sake lalen hukuncin zaben shugaban kasa na 2019, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasara.

Haka PDP ta bayyana a cikin wata takardar manema labarai da kakakin yada labarai na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya sa wa hannu a ranar litinin.

Sannan kuma PDP ta kara yin barazanar komawa kotu neman a sake shari’ar zabukan gwamnonin Katsina, Kaduna, Osun da na Kano.

Har ila yau, PDP ta zargi APC da kokarin zubar da kimar bangaren shari’a a kasar nan.

“Kowa ya san cewa APC ta dimauce ta shiga bankaura da hauraggiya, tun bayan kwace mata jihohin Zamfara da kuma Bayelsa.

“A dalilim haka babu ruwan su da martabar kotu ko Dalian kwace musu jihohin. Sun dimauce sai kokarin zubar da kimar fannin shari’ar kasar nan su ke ta yi, ta hanyar shigo da tsirfa da kutinguila daban-daban a bangaren shari’a.

“Idan haka ne, to ita ma PDP za ta koma kotu domin a sake bibiyar hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa da na gwamnaonin jihohin Katsina, Kano da kuma Osun.

Sai dai kuma kakakin yada labarai na APC, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana wa wakiinmu cewa PDP ta fama shirme.

Ya ce da su koma kotu neman soke zaben shugaban kasa da na gwamnonin Kano, Katsina da kuma Osun, har gara ma su su dauki fartanya su koma gona, su duka noma domin su samu abinci.

“Don PDP ta nemi komawa kotu, ai ba abin mamaki ba ne, domin babu abin da ake yi a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata House, a Abuja, sai zaman-kashe-wando kawai.”

Ya ce har yanzu ‘yan PDP na jimami da zaman takaicin subucewar mulki a hannun su. Shi ya sa masu zaman-dirshan suka yi kaka-gida a Wadata Plaza, hedikwatar PDP a Abuja.

Share.

game da Author