HARKALLAR NAIRA MILYAN 400: Kotu ta daure Kakakin PDP, Metuh shekara 39

0

Mai Shari’a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya daure tsohon kakakin yada labarai na jam’iyyar PDP, Olisah Metuh shekaru 39 a kurkuku.

An same shi da laifin karbar naira milyan 400 daga hannun Sambo Dasuki, kuma ya karkatar da kudin.

Metuh dai ya ce bai aikata laifin komai ba.

Alkali ya ce ya yarda Metuh ya yi laifi, saboda ya san kudin ba na jam’iyyar PDP ba ne, daga aljihun gwamnati Dasuki ya ba shi kudaden.

An same shi da laifuka 7. A laifi na daya an daure shi shekara 7. Laifi na 2 an daure shi shekara 7. Sai kuma daurin shekara 5 a laifi na 3.

An daure Metuh shekara 7 a laifi na 4. An sake daure shi shekara 3 a laifi na 5.

A laifi na 6 ne aka ce kamfanin Metuh, mai suna Destra Investment Ltd zai biya gwamnati naira milyan 25.

Sai kuma 7 ne aka daure Metuh shekara 7, tare da umartar sa ya biya naira milyan 375, a cikin asusun gwamnatin tarayya.

Zai fara zaman kurkukun wadannan dauri daya yau Talata.
Sai dai kuma a kowane kwana daya, ya yi wa kowace tuhuma kwanan kurkuku daya kenan.

Wato shekaru 6 kadai zai shafe a kurkuku.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kama tsohon Kakakin Yada Labarai na Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh da laifin karbar kudi gwamnati.

An same shi da kamfanin sa mai suna Destra Investment Ltda a laifin karbar naira milyan 400 daga ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa na Lokacin Goodluck Jonathan, Samabo Dasuki.

Mai Shari’a ya ce Oliseh ya san cewa kudin gwamnati ne aka gabza aka ba shi, kuma ya kamata ya san cewa kudin laifi ne ya aikata karbar kudaden.

Ana zargin sa ne da aikata laifuka bakwai da suka hada da karkatar da kudaden da Sambo Dasuki ya ba shi.

Cikin watan Fabrairu, Metuh ya bayyana wa kotu cewa shi bai aikata laifin komai ba.

Sannan kuma an zarge shi da karbar dala milyan 2 wuri-na-gugar-wuri, kai-tsaye ba tare da bi ta banki ba.

Bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari, an kama mutane da yawa da aka zarga da karbar kudade a hannun Dasuki, ciki kuwa har da tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa, Musuliu Obanikoro da wasu da dama.

Share.

game da Author