Duk da cewa Babbar Kotun Tarayya a Kano ta haramta wa Hukumar Sauraren Korafe-korafen Cin Rashawa ta Jihar Kano ta fitar da sakamakon binciken Sarki Muhammadu Sanusi II, sai kuma ga shi ta fito da wata hanyar da ta ce za ta ci gaba da aikin na ta.
Kotu dai ta ce ba daidai ba ne a fito da sakamakon binciken, domin ba a ji ta bakin Sarki ba. Don haka ba a yi masa adalci ba, a kan zargin salwantar naira bilyan 3.4 da ake yi wa Masarautar Kano.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji-Rimingado, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya saw a hannu, kuma ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a cewa za su fito da wani salon binciken da ya ce bai saba wa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a mako da ya gabata ba.
“Hukumar ta karbi sakamakon hukuncin da Babbar Kotu Tarayya ta Kano ta yanke, a ranar Juma’a, 21 Ga Fabrairu, 2020, a kara mai lamba FHC/KN/CS/102/2019.
Ya ce Sarki Sanusi ya je kotu ya nemi a haramta sakamakon bincike a ranar 31 Ga Mayu, 2019.
Kuma kotu ta amince cewa ta haramta binciken a kan ikirarin ta na rashin adalcin jin ta bangaren wanda ake bincike.
Ya ce ai kotu ba hana a binciki sarki ta yi ba. Ta dai haramta wancan sakamakon binciken ne saboda rashin jin ta bakin sa.
Kotu dai bayan ta haramta sakamakon, ta kuma umarci a biya Sarki Sanusi ladar naira 200,000.
‘Mun yi nazarin hukuncin Babbar Kotun Tarayya a karkashin Mai Shari’a O.A Egwuata, kuma mun fahimci ba wai binciken ya hana ba. Kenan za a iya fitar da wani sakamakon bayan an saurari ta bangaren wanda ya kai karar.
“Saboda haka wannan kwamiti ya na da zabi biyu: Na farko ko dai ya daukaka kara, saboda akwai dalilan daukaka karar.
“Na biyu kuma, ko a ci gaba da binciken, sai a gayyaci sarki domin bin umarnin kotu cewa ba a ji ta bakin sa ba.” Inji Magaji.