‘Yan bindigar Katsina sun sake damka wa Gwamna Masari mutane 30

0

‘Yan bindigar Katsina sun sake sako mutane 30 da suka yi garkuwa da su. Sun sako su ne a bisa yarjejeniyar da cimma da gwamnatin Jihar Katsina da kuma shugabannin su.

Jiya lahadi ne suka kai wa Gwamna Masari wadanda suka saki din har cikin Gidan Gwamnati.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda aka saki din an yi garkuwa da su bayan an kama su a Karamar Hukumar Kankara da kuma kauyen Shimfida da ke cikin Karamar Hukumar Jibiya.

Bayan an kama su ne aka yi awon gaba da su a Dajin Dansadau da ke cikin Jihar Zamfara, inda suka shafe makonni da dama a tsare.

Da ya ke wa wadanda aka saki din jawabi, Masari ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da lallashin ‘yan bindigar har sai sun saki dukkan mutanen da suka yi garkuwa da su.

Daga nan sai ya bada umarni a gaggauta kai su asibiti domin a binciki lafiyar su, kafin a mika su ga iyalan su.

Daga daga cikin wadanda aka sako din mai suna Zinatu Sani, ta shaida wa manema labarai cewa daga gidan aure aka sungume ta a yankin Kankara aka gudu da ita da ‘ya’yan ta biyu.

Zinatu cewa ta yi da farko naira milyan 20 masu garkuwar suka nema kafin a sake su. Daga bisani kuma suka nemi naira milyan 6, amma duk ba a samu ba.

“Mun shafe kwanaki 55 mu na kwanciya a fili, babu daki babu wata rumfa. A haka ruwa ke dukan mu. Su na ba mu shinkafa zalla da ruwa da gishiri mu dafa.

Daga nan sai Zinatu Sani ta gode wa Gwamna Masari da yi kokarin da ya kubutar da su.

An dai damka wadanda aka kubutar din ga Shugabannin riko na Kananan Hukumomin Kankara da Jibiya.

Share.

game da Author