Jami’an Hukumar EFCC sun bayyana damke Darakta-Janar na Hukumar Sokoto Marshall Agency, mai suna Abdullahi Sa’idu, bisa zargin karkatar da naira milyan 10 daga albashin ma’aikata.
Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar wa manema labarai daga Ofishin Shiyyar EFCC da ke Sokoto, ta bayyana cewa a ranar Asabar aka kama Darakta-Janar din tare da Babban Akanta na hukumar mai suna Bashir Dodo-Iya, wato ranar 13 Ga Satumba.
Sanarwar ta ce an cukume su ne bayan da aka gabatar wa EFCC da rubutaccen korafi dangane da yadda suka karkatar da albashin watanni uku na wadanda suka kai korafin.
Ma’aikata 39 suka hadu suka rubuta takardar korafin zuwa ga EFCC. Duk wani kokarin a biya su kudin sai da suka yi, bayan abin ya ci tura ne, sai suka garzaya EFCC dauke da takardar da kowanen su ya sanya wa hannu.
Sun ce an rike musu albashi na watanni uku, alhali kuma sun san gwamnati ta biya albashin, biyan su ne dai ba aka ki yi.
Masu korafin sun ce duk wani kokari da suka yi domin a biya su albashin natsaron watanni uku ya ci tura, sai suka garzaya EFCC.
“Binciken farko da EFCC ta gudanar ya nuna cewa jami’an biyu sun hada kai sun karkatar da naira milyan 10 domin biyan albashi na jami’an Marshall a Sokoto.
Sanarwar ta kuma kara da cewa wadanda ake zargin za su fuskanci tuhuma a gaban kotu.
Discussion about this post