GUMURZU: Yadda sojoji suka fatattaki Boko Haram a Jami’ar Maiduguri

0

Cikin daliban Jami’ar Maiduguri ya duri ruwa kuma sun firgita sosai a jiya Lahadi da dare, yayin da sojoji suka yi gumurzun fatattakar Boko Haram kusa da jami’ar.

Majiya daga cikin jami’ar ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an rika jin rugugin karar bindigogi na tashi a can bangaren da dakunan kwanan dalibai mata su ke.

An ce an shafe awa daya da rabi ana bata-kashi kafin sojoji su ci galabar korar Boko Haram.

Haka shi ma wani babban soja a Maiduguri ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram ne suka kai hari, amma sojoji suka fatattake su.

Dalibai wadanda ke tsakiyar zangon karatun su na biyu sun firgita sosai, tsoron kada Boko Haram su yi mus shigar-kutse a cikin makarantar. Hakan ya sa da dama sun yi kokarin tserewa daga jami’ar wadda ke kan Titin Maiduguri zuwa Bama.

“Amma sojoji da sauran jami’an tsaron da ke gadi makarantar suka ce kada kowa ya fita. Saboda duk wanda ya fice, idan ya ga babu wurin guduwa, to ba kuma za a bari ya sake dawowa cikin makarantar ba.”

Haka wata majiya a cikin jami’an tsaron makarantar ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Wata daliba mai suna Victoria, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa “a kusa da gidan kwanan mu mai suna B.0.T aka rika yin rugugin harbe-harben. Shi ya sa mu ka firgita sosai.”

Kadhija Muhammad da ke zaune a gidan dalibai mata mai suna Gidan Aisha Buhari, cewa ta yi “Kusa da gidan mu aka rika yin harbe-harben. Dukkan mu sai muka kwakkwanta a kan daben daki, mu ka yi shiru. An kai awa daya da rabi ana harbe-harbe, kafin can wajen karfe 11 na dare komai ya lafa.”

Share.

game da Author