Yadda Sanata Abbo ya yi sa-in-sa da Kwamitin Majalisar Dattawa

0

Jiya Talata ne Sanata Elisha Abbo ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa da aka kafa domin binciken abin da ake zargin sa da aikatawa.

An zargi Abbo da gag-gaura wa wata matar aure mai jego mari a a wani kantin sayar da azzakarin roba da sauran kayan da lalatattun maza da mata ke amfani da su domin gamsar da kan su sha’awa da jarabar jima’i.

Sai dai kuma a zaman kwamitin, ba a wanye lafiya da Abbo ba, wanda aka yi, aka yi da shi ya rantse kafin ya fara bayani cewa zai fadi gaskiya. Amma ya tubure, ya ki rantsewa.

Sannan kuma ya ki yarda ya yi magana a gaban ‘yan jarida.

A tsarin Majalisar Dattawa, duk wanda aka kira a ji bayanin sa ko ya bayar da shaida, sai ya yi rantsuwa kafin ya fara fadin bayanan sa.

Wannan ta sa an yi cacar baki mai zafi tsakanin mambobin kwamitin da kuma Abbo, wanda ya jajirce cewa sai ya fara yi wa kwamiti bayani tukunna kafin ya rantse.

Daga daga cikin mamba din kwamitin, wato Oluremi Tinubu, ta tsaya lallai sai Abbo ya yi rantsuwa tukunna, shi kuma ya ce babu wanda ya isa ya tilasta shi rantsewa.

Abbo ya kara da cewa bai ga dalilin da za a kirawo shi a ce ya rantse, sannan kuma ya yi bayanin batun da ya na kotu ba.

“Wannan rigima ta na kotu. Ba zai yiwu na rika magana ana dauka ta da kyamara a na rikodin din duk abin da na fada ba. Wannan yi wa kotu shisshigi ne.” Inji Sanata Abbo.

Nan da nan a cikin fushi, Oluremi ta shaida masa cewa: “Sanata kai fa sabon-yanka-rake ne, yanzu ka shigo Majalisa, kuma a nan ka same mu. Mu na da tsarin mu kuma a karkashin doka mu ke. Ba zai yiwu ka shigo yau din nan ba, sannan kuma ka ce kai ga yadda ka ke so mu yi abin da ya kamata mu yi.” Inji Sanata Oluremi, matar Bola Tinubu.

“A yanzu ka na wani matsayi ne. Kowa na bukatar a ji ta bakin sa tukunna, domin a yi adalci. Abin da ke faruwa a yanzu ya shafe ka kai kan ka. Dalili kenan Shugaban Majalisar Dattawa ya kafa kwamitin bincike.

“Shin ka na so mu mara maka baya ne mu goyi bayan ka, ko kuwa ka na so ne mu kare ka…. shin ba ka san cewa za mu iya dakatar da kai daga shigowa majalisa ba ne?” Inji Oluremi.

Nan da nan a fusace sai Sanata Abbo ya maida martani: “Ni fa ba zan zauna a nan ina sauraren ku ku na yi min barazanar dakatar da ni ba. Ni ma fa Sanata ne kamar kowanen ku. Ba za ku iya yi min kurari ko wata barazana da kokarin dakatar da ni ba.”

Bayan kura ta lafa daga hayaniyar da ta kaure ta dan wani lokaci, kwamitin ya bukaci ‘yan jarida su fita daga dakin zaman kwamitin.

Sai bayan da Sanata Abbo ya yi rantsuwa kuma ya bayyana ba’asin abin da ya faru a kantin sayar da azzakarin roba, sannan aka sake kirawo ‘yan jarida domin su sake shiga dakin zaman kwamitin.

Bayan wani lokaci kuma sai Shugaban Kwamitin, Sanata Sam Egwu ya shaida wa manema labarai cewa Abbo ya bayyana musu abin da ya faru, kuma ya ma kara fadar wasu abubuwan da kyamara ba ta nuna ba.

Ya kara da cewa sun kuma yi masa tambayoyi ya kuma amsa. Sannan kuma sun tambaye shi mutanen da za su iya zuwa domin su bayar da shaida.

“Mun kuma kira wadda aka gag-gaura wa marin, amma har yanzu ba mu ga shigowar ta ba. An ce manta ba ta jin dadin jikin ta. Amma dai nun ce ta zo ta same mu.

“A gobe kuma za mu gayyato duk wadanda za su bayar da shaida. Kama daga mai kantin, wadda aka mara, dan sanda da abokan kowa da ke wurin domin su bayar da shaida. Kuma a bayyane za a yi komai a gaban ‘yan jarida.”

Share.

game da Author