An kashe ‘Yan shi’a biyu,’Yan sanda biyu sun samu raunin harbin bindiga a arangamar Majalisa

0

Akalla ‘Yan shi’a biyu ne suka rasa rayukan su a arangamar su da jami’an ‘Yan sanda a majalisar Kasa dake Abuja, Najeriya ranar Talata.

Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne daruruwar ‘yan shi’a suka dunguma zuwa majalisar kasa a Abuja domin ci gaba da zanga-zangar da suke yi na yin kira ga gwamnati da ta saki shugaban kungiyar dake tsare.

‘Yan shi’an sun farfasa motocin a kofar shiga majalisar bayan ‘yan sanda sun hana su shiga cikin harabar majalisar sannan sun kona motan wani bakon majalisar da bai ci ba bai sha ba.

Rahotanni kuma sun nuna cewa baya ga fashe-fashen da suka yi sun harbi wasu ‘yan sanda biyu a arangamar.

Baya ga haka rundunar ‘yan sanda sun bayyana ce sun kama ‘yan shi’a 40 a wannan arangama.

Share.

game da Author