SHARI’AR ZABEN SHUGABAN KASA: PDP ta yi ikirarin kayar da APC a Jihar Katsina

0

Mai bada shaida na jam’iyyar PDP ya yi zargin cewa jam’iyyar su ce ta lashe zaben shugaban kasa a jihar Katsina.

Haka ya furta a lokacin da ya ke gabatar da shaida a yayin da ya ke amsa tambayoyin daga lauyoyin APC, a gaban Alkalan Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa a Abuja, jiya Talata.

Ya kara shaida wa kotun cewa shi bai ma yi zabe da katin zabe ba a lokacin da ya jefa kuri’a a zaben shugaban kasa na Fabrairu da ya wuce.

Yusuf, wanda ya bayyana cewa shi ne shugaban jam’iyyar PDP a jihar Katsina, ya yi zargin cewa jami’an zaben da ya kamata a ce su ne suka karbi korafe-korafe daga kananan jami’an zabe, duk tilasta su aka yi suka fice daga rumfunan zabe a lokacin zaben.

Wannan ikirari da ya yi, duk ya yi ne a kokarin san a tabbatar wa kotu cewa an tafka magudi a lokacin zaben.

Sannan kuma ya ce PDP, wato Atiku kuri’a 905,000 ya samu, shi kuma Buhari na APC ya samu 872,000.

Haka kuma wani mai gabatar da shaida mai suna Salisu Funtua, wanda ejan ne na tattara sakamakon zabe, ya rika karanto wata takarda a kotun, wadda ke dauke da bayanan da ya ce ya gabatar a matsayin korafin yadda aka rika yin magudi a wasu rumfuna, abin da ya janyo har aka soke zaben w=rumfuna biyu.

Share.

game da Author