Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya karyata rahotannin da aka buga cewa yace a cikin wannan makon ne Shugaba Muhammadu Buhari zai aika sunayen ministocin sa a Majalisar Dattawa.
Lawan ya musanta haka ne a jiya da dare, bayan fitowar sa daga taro da shugaba Buhari a Fadar Gwamnatin Tarayya.
Jim kadan bayan fitar ta sa, ya shaida wa manema labarai na Gidan Gwamnati cewa shi bai ce tabbas a wannan makon ne Buhari zai aika wa Majalisar Dattawa sunayen ministoci ba.
Ya ce wani Sanata ne ya yi magana cewa ya kamata Buhari ya aika musu da sunayen ministoci, domin mun kusa tafiya hutu.
“Ni kuma na ce masa bangaren gwamnati na nan na aiki tukuru a kan fitar da sunayen, wadanda mai yiwuwa ma a aiko mana da su a cikin wannan makon.”
“Don haka ni cewa na yi “mai yiwuwa a iya kawowa cikin wannan makon. Ban ce tabbas za a aiko mana a cikin wannan makon ba.”
A wurin taron dai Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa bai ma san akasarin ministocin da ya nada a 2015 ba, kuma bai san sahihanci da nagartar su ba kafin ya nada su.
Ya ce mafi yawan su duk jam’iyya ce ta ba shi sunayen su, wasu kuma daidaikun jama’a ne suka na shi sunayen suka nemi a nada su ministoci.
Buhari ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya karbi shugabannin Majalsar Tarraya da na Dattawa a taron sun a farko bayan zaben shugabannin majalisar.
A wurin taron, Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa amma a yanzu ba zai nada mutumin da bai sani ba, ya ba shi mukamin minista.
A taron san a farko da ya yi da shugabannin Majalisar Tarayya, Buhari ya ce sai wadanda ya amince da sahihancin nagartar su ne kadai zai nada mukamin minista. Kuma wadanda ya tabbatar da cewa za su iya gudanar da nauyin ayyukan da aka dora musu.
A taron wanda ya gudana a sabon dakin taron Fadar Shugaban Kasa, jiya Alhamis da dare, Buhari ya ce ya na fama da matsin-lambar ya nada ministoci.
Sai dai kuma ya kara da cewa, duk da wannan matsin-lamba da ya ke fama da ita, ba zai nada kowa ba sai wadanda ke da tarihin gudanar da ayyuka nagartattu, sahihai kuma mutane nagari.
“Da yawan mutane da ke nan zaune wurin wannan walimar na son ganin sunayen ministoci na, wanda hakan zai sa su tafi hutun su cikin kwanciyar hankali.
“To du kina sane da wannan; kuma ina cikin matsanancin matsin-lambar nada ministoci. Amma fa ministocin da na nada a wancan zango, akasarin su ban ma san su ba. Na amince da sunayen ne dai kawai wadanda jam’iyya da kuma wasu daidaikun jama’a su ka ba ni.
“Na yi aiki tare da su a tsawon shekaru uku da rabi. Mu na taro akalla sau biyu a sati. Kenan na san su sosai a yanzu.
“Amma a wannan lokacin, ni ne zan zabi ministoci na da kai na. Wato abin da na ke nufi, shi ne sai wadanda na sani gar-da-gar kadai zan nada ministoci.”
Daga nan Buhari ya yi kira ga ‘yan Majalisa da su hada hannu da bangaren gwamnati domin gina gwamnati tagari, wadda za ta bar ayyukan alherin da ta gina ko bayan shudewar ta.
Daga na kuma ya shawarci Majalisar Tarayya da ta Dattawa su daina kwatanta tsarin majalisar su da ta kasashen da suka ci gaba, irin su Amurka da Ingila.
Cikin wadanda suka je taron da Shugaba Buhari, har da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, Mataimakin sa Omo-Agege, Kakain Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila da Mataimakin sa Idris Wase.