Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa ba zai nada mutumin da bai sani ba, ya ba shi mukamin minista.
A taron san a farko da ya yi da shugabannin Majalisar Tarayya, Buhari ya ce sai wadanda ya amince da sahihancin nagartar su ne kadai zai nada mukamin minista. Kuma wadanda ya tabbatar da cewa za su iya gudanar da nauyin ayyukan da aka dora musu.
A taron wanda ya gudana a sabon dakin taron Fadar Shugaban Kasa, jiya Alhamis da dare, Buhari ya ce ya na fama da matsin-lambar ya nada ministoci.
Sai dai kuma ya kara da cewa, duk da wannan matsin-lamba da ya ke fama da ita, ba zai nada kowa ba sai wadanda ke da tarihin gudanar da ayyuka nagartattu, sahihai kuma mutane nagari.
“Da yawan mutane da ke nan zaune wurin wannan walimar na son ganin sunayen ministoci na, wanda hakan zai sa su tafi hutun su cikin kwanciyar hankali.
“To duk ina sane da wannan, kuma ina cikin matsanancin matsin-lambar nada ministoci. Amma fa ministocin da na nada a wancan zango, akasarin su ban ma san su ba. Na amince da sunayen ne dai kawai wadanda jam’iyya da kuma wasu daidaikun jama’a su ka ba ni.
“Na yi aiki tare da su a tsawon shekaru uku da rabi. Mu na taro akalla sau biyu a sati. Kenan na san su sosai a yanzu.
“Amma a wannan lokacin, ni ne zan zabi ministoci na da kai na. Wato abin da na ke nufi, shi ne sai wadanda na sani gar-da-gar kadai zan nada ministoci.”
Daga nan Buhari ya yi kira ga ‘yan Majalisa da su hada hannu da bangaren gwamnati domin gina gwamnati tagari, wadda za ta bar ayyukan alherin da ta gina ko bayan shudewar ta.
Daga na kuma ya shawarci Majalisar Tarayya da ta Dattawa su daina kwatanta tsarin majalisar su da ta kasashen da suka ci gaba, irin su Amurka da Ingila.
Shi kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, ya musanta rahotannin da aka buga cewa ya ce majalisa na jiran tsammanin karbar sunayen ministoci daga hannun Shugaba Buhari a cikin wannan makon.
Ya yi wannan kalamin ne bayan fitowar su daga ganawa da Buhari a taron na su na cikin dare a jiya Alhamis.
Ya ce wani Sanata ne ya yi magana cewa ya kamata Buhari ya aika musu da sunayen ministoci, domin mun kusa tafiya hutu.
“Ni kuma na ce masa bangaren gwamnati na nan na aki tukuru a kan fitar da sunayen, wadanda mai yiwuwa ma a aiko mana da su a cikin wannan makon.”
“Don haka ni cewa na yi “mai yiwuwa a iya kawowa cikin wannan makon. Ban ce tabbas za a aiko mana a cikin wannan makon ba.”
Cikin wadanda suka je taron da Shugaba Buhari, har da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, Mataimakin sa Omo-Agege, Kakain Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila da Mataimakin sa Idris Wase.