Kotu ta raba auren magidancin da sai ya ba matarsa cin hanci kafin ta yarda ya kwana da ita

0

Kotun Igando dake jihar Lagas ta warware auren shekara 16 dake tsakanin Risikat da Adeniyi Adeboyega a dalilin kauracewa Adeniyi da Risikat ta yi a gado.

Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya yanke hukuncin haka ranar Alhamis.

Koledoye ya kuma raba ‘ya’ya hudu da Adeniyi da Risikat suka haifa sannan Adeniyi zai rika biyan Naira 10,000 duk wata kudin abincin yaran dake hannu Risika.

Sannan ya biya Naira 200,000 wa Risikat domin ta ci gaba da rayuwarta.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Adeniyi ya shigar da kara a kotu cewa a duk ranar da da bukaci ya kwana da matar sa sai ta bukaci ya biya ta kudi tukunna kafin ta yardan masa.

Adeniyi ya kuma koka da cewa matarsa Risikat mafadaciya ce sannan bata dafa abinci a gidan.

Ya roki kotu da ta raba auren su kowa ya huta.

Ita kuwa Risikat ta musanta duk abin da Adeniyi ya fada a kanta domin ta bayyana cewa Adeniyi kan lakada mata dukan tsiya a duk lokacin da ta yi masa laifi.

“ Adeniyi matsafi ne domin ya yi mun asirin da ya sa ni rashin lafiya. Sannan Adeniyi ya kore ni da ‘ya’yan mu daga gidan mu na tsawon watanin tara.”

Risikat ta roki kotu da kada ta raba auren domin har yanzu tana son mijinta.

Share.

game da Author