Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa cutar kwalara ta bullo a jihohin Adamawa da Katsina.
Mutane 64 ne suka kamu da cutar a kananan hukumomi bakwai a wadannan jihohi.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu, ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba a Abuja.
“ Gwajin da muka yi ya tabbatar mana da cutar a jikin mutane takwas sannan mutum daya rasa.
“A lissafe dai mun gano cutar a jikin mutane 40 a jihar Adamawa sannan 24 a jihar Katsina.
Ihekweazu ya ce ma’aikatan su na iya kokarin su wajen ganin sun dakile yaduwar cutar amma yana kira ga gwamnatocin jihohin da kungiyoyin bada tallafi kan hada hannu da su domin wayar da kan mutane mahimmancin tsaftace muhalin su.
“Za iya yin haka ne ta hanyar saka talla a gidajen yada labarai da tarurruka.
ZAZZABIN LASA
Ihekweazu ya kuma sanar cewa zazzabin lassa ya bullo a jihohi 10 a kasar nan.
Jihohin da cutar ta bullo sun hada da Edo, Ondo, Ebonyi,Plateau,Adamawa, Gombe,Benue, Kebbi, Bayelsa da babban birnin tarayya Abuja.
“Mun gano cutar ne a jikin mutane 65 a kananan hukumomi 18.
“Gwajin da muka yi ya tabbatar mana da cutar a jikin mutane biyu sannan mutum daya ya mutu.
BAKON DAURO
Ihekweazu yace bakon dauro ya bullo a duk jihohin dake kasar nan.
Ya ce an samu rahoton akalla mutane 805 na dauke da cutar sannan mutane hudu sun rasu.