Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa alhakin ilmantar da milyoyin yaran da ke yawon almajirci ya rataya ne a wuyan gwamnoni.
“Su ma jihohi na da masu ilmi da masu fada-a-ji wadanda ke da ilmin da za su tunatar kuma su fadakar da gwamnonin su dangane da nauyin da ke wuyan su a kan matsalar almajirai.”
Haka Buhari ya bayyana a lokacin da ya karbi bakuncin Shugabannin Kungiyar Likitoci ta Kasa a Fadar Gwamnatin Tarayya.
Kakakin Fadar Shugaban Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya fitar da sanarwa dangane da wainar da aka toya a lokacin ziyarar.
Ya ce Buhari ya shaida musu cewa batun samar da kiwon lafiya da ilmi, abu ne da dokar kasa ta tilasta shi.
“Idan akwai tulin almajirai a jiha, to kenan gwamnati ba ta bin tsarin doka kenan.”
Dokar Najieriya dai ta wajibta samar wa yaro ilmi tun daga firamare har kammala karamar sakandare kyauta.
Akasarin yaran da ke barace-barace a kan titi da lungunan Arewacin kasar nan, duk wadanda ba a dauke su zuwa makarantu ba ne.
Idan ba a manta ba, gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta kashe bilyoyin nairori wajen gina makarantun da za a rika koya wa almajirai ilmin zamani da na addinin Musulunci a fadin Arewacin kasar nan.
Tsarin da a ka yi a lokacin shi ne a rika samar musu da ilmin zamani ta hanyar koyar da su karatun zamani da na addini a cikin ajujuwa.
A lokacin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya ce akalla akwai almajirai milyan 9.5 masu gararamba a kan titinan kasar nan.
Dukkan wadannan almajiran kuwa babu wanda ke zuwa karatun zamani.
Sai dai kuma shirin bai samu karfin guiwa da, duk kuma da cewa an tsara yadda za a ci moriyar sa.
Gwamnatin Buhari ba ta ci gaba da shirin ba, ta yadda a yanzu an kiyasta almajirai a Arewa sun kai milyan 13.2.
Da yawan ‘yan Najeriya na kukan cewa a hana almajirci, domin ya na haifar da masu tsatstsauran ra’ayin akidun da a karshe su ke komawa ta’addanci.
Ko a kwanan baya sai da gwamnatin Buhari ta yi sanar da hana barace-barace da almajirci, amma kuma ta ce ba a yanzu-yanzu ba, sai a hankali.