Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta gayyaci Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kuma Kwamishinan Zabe na Jihar Zamfara.
Kotun ta bukaci su bayyana a gaban ta gobe Alhamis kafin karfe 12 na rana.
Kotun ta bayar da wannan umarni a yau Laraba, biyo bayan wani korafi da jam’iyyar PDP ta yi cewa INEC a tarayya da kuma jihar Zamfara ta ki bin umarnin kotu ta ba su a ranar 12 da 15 Ga Yuli.
Kotu ta ce ta na so tabbas shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya kai kan sa a kotun tare da Kwamishinan Zabe na Jihar Zamfara.
“ Tunda da dai takardun bayanai sun tabbatar da cewa an aika wa Shugaban INEC da Kwamishinan INEC na Zamfara takardar sanarwar cewa su bayar da kwafen bayanan da ake nema a wajen su.
“Don haka ya zama dole su da kuma lauyoyin da ke wakiltar su cewa su bi dokar kotu.
“Nauyi ya rataya a wuyan su lallai su bi doka.” Inji kotu.
Kotun wadda Mohammed Garba ke shugabanta, ta bayar da wannan umarnin gayyatar su ne bayan da lauyoyin PDP suka shaida mata cewa sun tura musu musu takardun neman bayanai tun a ranakun 12 da 15 Ga Yuli, amma shiru har yau ba su ce komai ba.
Wannan gayyata da kotu ta yi ta na daga ci gaba da sauraren karar zaben shugaban kasa wanda Atiku da PDP suka maka APC, INEC da Buhari kotu, inda suke kalubalantar nasarar da INEC ta bayyana cewa APC da Buhari sun yi.
Discussion about this post