IYA RUWA FIDDA KAI: Yadda Goje ya tsallake EFCC, Ofishin AGF cikin ruwan sanyi

0

Abu kamar almara yau wai sai gashi cikin kwanaki kadan an wanke tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje da aka yi ta kai ruwa rana tsakaninsa da hukumar EFCC har na tsawon shekara takwas ana fafatawa.

Da yake ya iya takunsa cikin ruwan sanyi Goje yanzu zai kakkabe babban rigarsa ya kule dakinsa cikin ruwan sanyi ba tare da wani ya saje ce masa uffan ba.

Yadda janye takarar shugabancin majalisa ya hada kan EFCC da Ofishin AGF, aka yafe wa Goje

Ga yadda akayi dalla-dalla

1 – Cikin 2012 ne EFCC ta gurfanar da Goje a kotu, inda aka tuhume shi da hadin-baki suka karkatar da zunzurutun kudade, shi da wani mai suna Aliyu El-Nafarty, sai Shugaban Hukumar UBEC ta Jihar Gombe na lokacin Goje, Sambo Tumu da kuma wani dan kasuwa mai suna S.M Dakuro.

2 – EFCC ta ce su hudu sun hada kai kuma sun hada baki sun karkatar da naira bilyan 25.

3 – Bayan an shafe shekaru takwas ana tafka kwatagwamgwamar shari’a, sai kotu a ranar 22 Ga Maris, 2019 ta soke tuhume-tuhume 19 da ake yi wa Goje daga cikin 21, aka bar biyu rak.

4 – Sai kuma EFCC ta janye hannun ta gaba daya daga tuhumar sauran cikon tuhuma guda biyu da suka rage a ke wa Goje, kwana daya bayan da Goje ya kai wa Buhari ziyara a Fadar Shugaban Kasa, inda ya bayyana cewa ja fasa yin takarar shugabancin Majalisar Dattawa tare da Sanata Lawan.

5 – Hakan ya sa jama’a sun rika cewa Gwamnatin Buhari ta yi wa Goje tukuici ne da soke shari’ar da ake yi masa, domin ya biya rigaya ya biya mata bukatar ta. Wato idan ungulu ta biya bukata, to zabo ya tafi da zanen jikin sa ba kawai.

6 – Ranar 21 Ga Yuni kuma sai Ofishin AGF ya ci gaba da gurfanar da Goje a Kotu, kamar yadda EFCC ta bayyana cewa ta tsame hannun ta, shi ofishin AGF ne zai ci gaba. Haka ta faru a Babbar Kotun Tarayya da ke Jos, inda ake tafka shari’ar.

7 – Daga nan sai aka dage sauraren karar zuwa ranar 4 Ga Yuli, domin lauyan Ofishin AGF mai suna Pius Akutah, ya nemi kotu ta dan ba shi lokaci ya je ya bi kadin yadda shari’ar ta kasance a baya.

8 – Yayin da aka koma kotu a ranar 4 Ga Yuli, sai lauyan Ofishin AGF ya sanar da kotu cewa, “Ma’aikatar Shari’a, wadda kuma ita ce Ofishin AGF din ta na sanar da kotu cewa ta janye dukkan tuhume-tuhume da suka rage guda biyu da ta gurfanar da Goje a kotu saboda su.”

9 – Shi ma lauyan Goje, Adeniyi Akintola bai yi wata ja-in-ja ba, ya ce ya amince a janye tuhumar da ake wa wanda ya ke karewa.

10 – Daga nan sai Mai Shari’a Babatunde Kadiri, ya ce ya yi amfani da Sashe na 174(1) musamman na (b) da kuma abin da Sashe na 108 (2) na Dokar 2015 ya shimfida, ya kori, karar, kuma an kashe maganar faufaufau.

Share.

game da Author