TA LEKO TA KOMA: Afrika Ta Kudu ta fidda kasar Masar

0

Kasar Afrika Ta Kudu ta fidda Kasar Masar a gasar cin kofin nahiyar Afrika da ake bugawa a kasar Masar.

Afrika Ta Kudu ta doke Masar da ci daya mai ban haushi.

Dan wasan kasar Afrika Ta Kudu ya zura wa Masar kwallo a raga ne minti biyar kacal a kammala wasan.

Wannan rashin nasara bai yi wa kasar Masar dadi ba ganin cewa suna suke karbar bakuntar wasan wannan shekara.

Najeriya da ta yi nasara akan kasar Kamaru da ci 3 -2 a wasan yamman ranar Asabar.

Najeriya zata kara a wasan kwata fanal da kasar Afrika ta Kudu.

Share.

game da Author