Ta tabbata dai Sanata Danjuma Goje bai yi asarar janyewa daga neman mukamin shugabancin Majalisar Dattawa da ya yi ba. Domin wannan dabara da ya yi, ta yi daidai da karin maganar da Hausawa ke cewa: “Hikima kashin-kwance, wai idan ka iya, to sai ka tula shi ba tare da ya bata maka jiki ba.”
Sai dai kuma shi Sanata Goje, kashin da ya tula ya bata masa jiki jabe-jabe, amma kuma Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta wanke masa jikin sa, ta saka masa sabbin kaya, har ma da bulbula masa turare.
Dalili, jiya Juma’a ne Ofishin Shugaban Shigar Da Kararrakin Gwamnatin Tarayya ya janye sauran tuhume-tuhume guda biyu rak da suka rage ake yi masa, daga tulin zargin cin rashawa, hanci, wawurar kudade da harkalla.
Nan take kotu ta amince da wannan janye karar da ake yi wa Goje tsawon shekaru takwas, inda ake tuhumar sa da lafin cika aljifan sa da naira bilyan 25 daga kudin gwamnatin jihar Gombe, a zamanin shekaru takwas da ya yi ya na gwamnan jihar.
Tun da farko dama EFCC ce ta fara bai wa duniya mamaki, inda ta bayyana a gaban kotu, ta ce ta janye karar da ta shigar da Sanata Goje, wadda aka shafe shekaru takwas ana tabkawa. Ta ce ofishin Antoni Janar na Tarayya ne zai ci gaba da gurfanar da Goje a kotu, ba EFCC ba.
Wannan asarkala da na-jen-je-ni kuwa ta faru kwana daya tak bayan Goje ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara, inda ya bayyana janyewa daga takarar shugabancin Majalisar Dattawa, ya ce ya bar wa wanda gwamnatin tarayya, Buhari da shugabannin APC ke goyon baya, wato Sanata Ahmed Lawan.
BA KUNYA BA TSORON BAKIN JAMA’A
Wannan kawance da EFCC da Ofishin Antoni Janar suka yi a batun shari’ar Goje, ya bai wa jama’a mamaki matuka. Domin dai kowa a kasar nan ya san cewa kafin hakan, Hukumar EFCC da wannan ofishin su na ’yar-tsama da junan su a batun yaki da cin hanci da rashawa. Wato kowace ofishi ya na zargin daya ofishin da yin rufa-rufa.
Yayin da ofishin Antoni Janar ke zargin EFCC da wuce makadi-da-rawa, ita kuma EFCC na zargin ofishin Antoni Janar da kasa yin katabus da kuma rashin kuzarin iya yaki da cin hanci da rashawa.
YADDA EFCC DA OFISHIN ANTONI JANAR SUKA RIKA KWANCE WA JUNA ZANI A KASUWA
Akwai misalai da dama inda EFCC ta rika tafka rigima da Ofishin Antoni Janar a kan wasu kararrakin da ke gaban kotu. Akwai lokacin da a cikin Nuwamba 2018, ofishin ya nemi karbe shari’ar da EFCC ta gurfanar da John Abebe, wani dan uwan Stella Obasanjo, a kotun Lagos, amma EFCC ta ki amincewa.
Akwai kuma wani lokaci a cikin watan Maris, 2016, EFCC da Ofishin Antoni Janar suka rika tafka rikici a Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, dangane da wanda zai gurfanar da wasu mutane 16 da ake tuhuma da harkallar naira bilyan 43 ta ’Consolidated Discount House Limited.’
Duk da a ranar 23 Ga Fabrairu, 2016, sai da ta kai Babban Mai Shari’a Mohammed Idris ya ce su je su sasanta junan su a kan wanda zai gurfanar da wadanda ake zargin, amma abin ya faskara.
Lauyan EFCC A.B.C Ozioko, ya jajirce a gaban alkali cewa EFCC c eke da hakkin ci gaba da gurfanar da wadanda ake tuhumar, tunda su na tsare a hannun ta.
Ko a cikin 2017 sai da EFCC da ofishin AGF suka tafka kitimirmirar kokawar kwace wa juna gurfanar da wasu da ake zargi da aikata harkalla.
Haka nan kuma sun kunyata junan su a lokacin da aka zargi Shugaban Kotun CCT, Danladi Umar da karbar rashawa.
Sannan kuma a rikici da shari’ar harkallar Malabu, nan ma EFCC da Ofishin AGF kowa ra’ayin sa daban.
Cikin 2018 Ofishin AGF dai ya shawarci Shugaba Buhari a daina shari’ar Rijiyar Mai ta Malabu, mai lamba OPL 245, wadda aka tafka harkallar bilyoyin nairori a wurin cinikin ta. Sai dai kuma Buhari bai amince da wannan shawara ba.
Rijiyar OPL 245, rijiyar danyen mai ce wadda aka hakkake cewa akalla akwai danyen mai har ganga bilyan 9 kwance a karkashin ta, amma aka sayar da ita akan dala bilyan 1.3 kacal.
An yi zargin wadanda suka yi hada-hadar cinikin sun karbi cin hancin dala milyan 801 ta yadda suka sayar da rijiyar arha takyaf.
Daga baya Buhari ya umarci EFCC su gurfanar da duk wanda ke da laifi wajen wannan harkalla, wadda Ofishin Antoni Janar, AGF ya ce a hakura da bin shari’ar.
GOJE: ‘UNGULUN DA TA FI ZABO ZAKIN NAMA
Cikin 2012 ne EFCC ta gurfanar da Goje a kotu, inda aka tuhume shi da hadin-baki suka karkatar da zunzurutun kudade, shi da wani mai suna Aliyu El-Nafarty, sai Shugaban Hukumar UBEC ta Jihar Gombe na lokacin Goje, Sambo Tumu da kuma wani dan kasuwa mai suna S.M Dakuro.
EFCC ta ce su hudu sun hada kai kuma sun hada baki sun karkatar da naira bilyan 25.
Bayan an shafe shekaru takwas ana tafka kwatagwamgwamar shari’a, sai kotu a ranar 22 Ga Maris, 2019 ta soke tuhume-tuhume 19 da ake yi wa Goje daga cikin 21, aka bar biyu rak.
Sai kuma EFCC ta janye hannun ta gaba daya daga tuhumar sauran cikon tuhuma guda biyu da suka rage a ke wa Goje, kwana daya bayan da Goje ya kai wa Buhari ziyara a Fadar Shugaban Kasa, inda ya bayyana cewa ja fasa yin takarar shugabancin Majalisar Dattawa tare da Sanata Lawan.
Hakan ya sa jama’a sun rika cewa Gwamnatin Buhari ta yi wa Goje tukuici ne da soke shari’ar da ake yi masa, domin ya biya rigaya ya biya mata bukatar ta. Wato idan ungulu ta biya bukata, to zabo ya tafi da zanen jikin sa ba kawai.
Ranar 21 Ga Yuni kuma sai Ofishin AGF ya ci gaba da gurfanar da Goje a Kotu, kamar yadda EFCC ta bayyana cewa ta tsame hannun ta, shi ofishin AGF ne zai ci gaba. Haka ta faru a Babbar Kotun Tarayya da ke Jos, inda ake tafka shari’ar.
Daga nan sai aka dage sauraren karar zuwa ranar 4 Ga Yuli, domin lauyan Ofishin AGF mai suna Pius Akutah, ya nemi kotu ta dan ba shi lokaci ya je ya bi kadin yadda shari’ar ta kasance a baya.
Yayin da aka koma kotu a ranar 4 Ga Yuli, sai lauyan Ofishin AGF ya sanar da kotu cewa, “Ma’aikatar Shari’a, wadda kuma ita ce Ofishin AGF din ta na sanar da kotu cewa ta janye dukkan tuhume-tuhume da suka rage guda biyu da ta gurfanar da Goje a kotu saboda su.”
Shi ma lauyan Goje, Adeniyi Akintola bai yi wata ja-in-ja ba, ya ce ya amince a janye tuhumar da ake wa wanda ya ke karewa.
Daga nan sai Mai Shari’a Babatunde Kadiri, ya ce ya yi amfani da Sashe na 174(1) musamman na (b) da kuma abin da Sashe na 108 (2) na Dokar 2015 ya shimfida, ya kori, karar, kuma an kashe maganar faufaufau.
WATA SHARI’A SAI A LAHIRA?
Yayin da wasu ke ganin cewa Ofishin Antoni Janar na da ikon da zai kashe shari’ar, da dama kuma na ganin cewa ba daidai ba ne, domin shekara takwas aka yi ana tafka shari’a, kuma har mutane da dama sun je kotu sun bayar da shaida.
Shin tambayar da wasu ke ta yi wa junan su ita ce: Su Goje sun ci banza ne kenan? Ina batun sauran mutane uku da ake tuhumar Goje tare da su? Su ma gaba ta kai su kenan, wai gobarar-Titi. Shin wannan shari’a ta yi, ko kuma idan wata gwamnati ta hau za ta sake kakkabe fayil ta sake kamo Goje idan da rai da lafiya?
Ko kuwa dai shikenan, wata shari’a sai a lahira?