Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, ya yi tattaunawa ta musamman da PREMIUM TIMES, a cikin watan da ya gabata. Cikin batutuwan da ya yi magana a kai, har da batun matsalar garkuwa da jama’a, rikicin makiyaya da manoma, matsalar tsaro da kuma abin da za a yi zaman jira a gani ko samu daga zangon Shugaba Muhammadu Buhari na biyu:
ZARGIN GWAMNATI NA RAGA WA FULANI MAKIYAYA
“Ina ganin duk wanda zai zargi gwamnatin tarayya da raga wa Fulani makiyaya, ko goyon bayan su a rikicin su da mnoma, to gaskiya bai yi adalci ba. Sannan kuma irin yadda ake yi wa Fulani kudin-goro, an ace musu makiyaya, wannan ma kuskure ne. Yanzu ka ga ni makiyayi ne, amma ba Bafulatani ba ne.
“Don haka a nan Arewa idan aka ce dukkan Fulani makiyaya ne, to karya ce. Dukkan mu makiyaya ne, kuma monama ne. Wani noman sa shi ne kiwon dabbobi, wani kuma noma na shuka amfanin gona ya ke yi.
“Rikicin makiyaya da manoma ba sabon abu ba ne, kuma yankuna da dama su na da hanyoyin da ake bi sun a sananta juna tsakanin su.
“Wato a kasar nan mun rika yin abubuwa da dama wadanda daga baya kuma za su zame mana alakakai mu na ji mu na gani. Ka da dai duk an bi burtalolin da aka kefe wa makiyaya da dabbobin su, an nome, ko an gine, ko an maida su gonaki. Haka kuma aka yi wa dazukan kiwon da gwamnati ta kebe musu. Duk an maida su gonaki. Wannan kuma duk aikin manoman mu na zamani ne masu ilmi. Su aka damka wa wadannan wurare su na nomewa.
Babu wadataccen wuraren kiwo ko mashayar ruwan dabbobi, duk an killace su, an yi bango ko an kewaye da waya an yi musu shinge. Shi ma kiwon kifi duk ya ja baya. Haka makarantun da sojoji suka yi a cikin shekaru 1970s. ina magana shirin ilmantar da ‘yan’yan Fulani.
“A yanzu gwamnati na bakin kokarin ta. Za ta taimaka wa jihohin da a su kebe makiyayar dabbobi domin ganin sun gina wadannan wuraren kiwo.
YADDA FULANI SUKA ZAMA ’YAN BINDIGAR KARFI-DA-YAJI
Yin amfani da karfin sojoji a rikicin Arewa maso Yamma ba zai kawo karshen matsalar ba. Saboda ka ga dai kusan duk shanun da ke hannun Fulanin yankin wadanda ke cikin jeji, duk an sace musu shanun. Sai su kuma Fulanin aka bar su a cikin jeji suka koma kamar mahara masu samame.
“Ka ga kenan an bar Bafulatani a cikin daji, ana farautar sa bayan an sace masa shanu. Don haka rikicin Yankin Arewa maso Yamma ya na bukatar hada hannun gwamnati da al’umma domin a shawo kan sa. Shi ya sa na ke cewa idan ba mu yi da gaske ba, to rikicin garkuwa da jama’a sai ya fi na Boko Haram muni.
NASARAR BUHARI A KARO NA BIYU
“Wannan nasara ta daukar min hankali sosai, saboda sai da aka yi gumi sharkaf sannan aka same ta. Mun yi aiki tukuru a kamfen, domin ni ne daraktan kamfen da hada kan ‘yan jam’iyya. Mu na da yakinin a lokacin za mu ci zabe. To a zango na biyu kuma sai na fi mamaki, saboda ya ma fi samun rata mai yawa tsakanin sa da wanda ya kayar.
ABINDA ZA A JIRA A GANI DAGA BUHARI A ZANGO NA BIYU
Zan iya sha muku alwashin cewa akwai dimbin alheri tattare da wannan zango na biyu na Shugaba Muhammadu Buhari. Ya na da kishi da kyakkyawan kudirin inganta kasar nan, musamman yadda ya maida hankali wajen muhimman ajandojin nan na sa guda uku. Daga lokacin da muka kai shekara ta 2023, to na tabbata jama’a za su tabbatar da cewa Shugaba Buhari ya kai Najeriya tudun-mun-tsira ta yadda kowa zai yi alfahari da kasar nan.
Na tabbatar kuma tattalin arziknmu da albarkatun kasar mu sun karu ainun. Ana kuma samun kudaden shiga masu tarin yawa, ba kamar da ba. Don haka na tabbatar zai cika alkawurran da ya dauka, kuma ‘yan Najeriya ba za su yi da-na-sani ba a zangon sa na biyu.