Gwamnan jihar Kaduna ya kirkiro sabbin ma’aikatu har guda uku a jihar Kaduna.
Ma’aikatun da ya kirkiro sun hada da Ma’aikatan Kasuwanci da Fasaha sai kuma Ma’aikatan Gidaje da Tsara- Birane da Ma’aikatan Tsaro da Harkokin Cikin-Gida
Baya ga wadannan sabbin ma’aikatu da aka kirkiro an rusa wasu guda uku.
Wadanda aka rusa sun hada da Ma’aikatan Cinikayya da Masana’antu, sai kuma Ma’aikatan Ci gaban Karkara da Ma’aikatan Ruwa.
Sanarwar wanda kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ya saka wa hannu ya bayyana cewa har yanzu dai ma’aikatu 14 gwamnatin jihar Kaduna za ta yi aiki da su.
Akwai kuma Ma’aikatun da aka karawa ayyukan da za su rika yi wato an kara musu dawainiya.
Baya ga nan sanarwar ta ce da zaran majailisar jihar ta dawo za a mika mata sunayen kwamishinonin da gwamna ya zaba domin tabtancesu