Za a hukunta sojoji 14 bisa zargin kisa da garkuwa da mutane

0

Hukumar Sojojin Najeriya ta fara tuhumar wasu sojoji 14 da ake zargi da kisa. Garkuwa da mutane da kuma kauracewa daga wurin aiki.

Da ake kaddamar da fara tuhumar ta su a Fatakwal jiya Asabar, Babban Kwamandan Runduna ta 6 da ke Fatakwal, Jamil Sarham, ya ce dukkan wadanda ake tuhumar jami’an sojojin da ke rundunar ta sa ce.

Manjo Janar Sarham ya ce an shirya yi musu shari’a ne a karkashin dokar soja ta 131 wadda ta rattaba ka’idojin da hukumar sojoji za ta tuhumi kuma ta hukunta wadanda ta kama da laifi.

“Daga cikin tuhume-tuhumen da za a yi musu akwai zargin kisa, yunkurin kisa, garkuwa da jama’a da kuma kauracewa daga wurin aiki.

“Akwai kuma wasu laifukan da suka shafi rashin da’a da rashin bin umarnin da doka ta shimfida da kuma aikata wasu dabi’u da su a bisa turbar tsarin aikin sojoji.

Daga nan ya ce rundunar sojoji ba ta yarda da rashin da’a ba, kuma za ta taba boye mai laifi ta hana a hukunta shi ba komai girman mukamin sa.

Ya ce hukumar sojoji ta dauki jami’an ta da muhimmancin gaske, kuma ta na matukar girmama su. Don haka ba za ta taba yin gaggawar hukunta kowa ba, har sai ta yi kwakwaran binciken tabbatar da laifi ga wanda ake zargi tukunna.

Daga nan sai Sirham ya ce shari’ar da za a yi musu ba za a yi ta ne da nufin hukunta masu laifi kadai ba, har ma da zama darasi ga wasu domin su guji tsoma kan su cikin aikata laifuka.

Ya umarci kwamitin alkalan su bakwai da aka nada su yi hukuncin a karkashin Burgediya Janar Bassey Etuk su tabbatar da sun yi wa kowa shari’a mai adalci.

Daga cikin wadanda ake tuhumar su 14, akwai jami’ai uku da kananan sojoji 11 da suka hada da manjo daya, kaftin biyu da sauran su.

Share.

game da Author