Sojojin Najeriya suna sata da bumburutun danyen man fetur a Ribas –Gwamna Wike

0

Gwamna Nyesom Wike ya zargi Sojojin Najeriya da aikata harkallar bumburutun danyen mai a Jihar Ribas.

Gwamnan ya zargi Kwamandan Rundunar Sojoji ta 6, Manjo Janar Jamil Sarham da kafa wani gungun sojoji masu satar danyen man fetur su na sayarwa a yankin.

“Shi wannan Babban Kwamandan ya kafa wani gungun sojoji masu satar masa mai, saboda ya na so ya zama Babban Hafsan Askarawan Sojojin Najeriya.”

Haka Wike ya furta a lokacin da ya karfi bakuncin wasu manyan jami’an sojoji daga ‘Operation Delta Safe’, a ranar Labarar da ta gabata.

“Idan aka ba irin wannan mutumin Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, to wane irin tsaro ku ke jin zai samar?” Haka Gwamna Wike ya kara furtawa.

Har ila yau, Wike ya ce Manjo Janar Sarham ya na gulmata wa rikakkun masu laifi wasu bayanan sirri na tsaro.

Sannan kuma da gangan Hukumomin Tsaro na Sojoji su ka ki cire shi.

“Za mu je mu zauna mu yi taro a kan sha’anin tsaro, amma sai ya kwashe ya je ya sanar wa rikakkun masu aikata lafi.

Amma Babban Hafsan Askarawan Najeriya ya bar shi a nan, ya ki cire shi, saboda kawai da bazar su ya ke rawa.” Inji Gwamna Wike.

Ya ci gaba da cewa duk da irin kokarin da ya ke yi domin ganin a matsayin sa na gwamna ya dakile matsalar tsaro a jihar Rivers, abin takaici, sojoji na maida masa hannun agogo baya.

‘Operation Delta Safe’, runduna ce ta gamayyar jami’an tsaro daga bangarori, wadda akan kai wa rahotannin masu satar danyen mai da masu lalata wuraren hakar mai ko fasa bututu.

Sun kai wa gwamnan ziyara ce a karkashin Shugaban Rundunar, Real Admiral Akinjide Akinrinade.

Ya kuma kara da cewa zai yi wahala zaratan ‘Operation Delta Safe’ su iya kama sojojin Najeriya idan har suka ritsa su su na satar mai.

GWAMNA WIKE: Mai Tsoron Aradu Shi Ta Ke Fadawa…

Ba tun yau Gwamna Wike ya saba ragargazar sojojin Najeriya ba.

Bai dai bayar da wata hujja ba a bisa zargin da ya yi. Sannan kuma kakakin yada labaran sa, Oraye Franklin, ya shaida wa PREMIUN TIMES cewa babu wani abin da zai kara a kan bayanan da gwamnan sa ya yi.

Wike ya sake yin nasara a karkashin jam’iyyar sa, PDP. Ya sha yin kakkausan zargi a kan gwamnatin Buhari da jami’an tsaro.

Jim kadan bayan fallasa makudan kudaden da aka kimshe a wani gida a unguwar Ikoyi, Lagos, a cikin Afrilu, 2017, Wike ya fito ya ce kudin mallakar Jihar Rivers ne, wadanda ya ce tsohon gwamnan jihar, Rotimi Amaechi ya sace.

Sai dai kuma a lokacin bincike, ya kasa bada shaidar kudin na jihar sa ne. Daga baya sai Hukumar Leken Asiri (NIA) ta ce na ta ne. Daga nan aka maida su aljihun gwamnatin tarayya.

Ya kuma sha zargin gwamnati da jami’an tsaro, ciki har da ’yan sanda na kokarin kashe shi, amma dai ba ya bayar da hujjoji.

SAI AN BA NI UMARNI ZAN MAIDA RADDI- Manjo Janar Jamil

Ganin irin wannan babban zargi da Gwamna Wike ya yi wa Manjo Janar Jamil Sarham, kafin PREMIUM TIMES ta buga wannan labari, sai da ta nemi jin ta bakin sa tukunna.

Sai dai kuma abin da kawai ya furta, shi ne: “Wannan zargi ya yi muni sosai.” Sannan kuma ya kara da cewa bai kai ga samun umarnin maida martani ba tukunna.
Ya yi wa PREMIUM TIMES wannan bayani ne a yau safiyar Lahadi, karfe 9:20 na safe.

Shi kuma kakakin yada labarai na sojoji na kasa, Sagir Musa, bai yi karin bayani ba, a lokacin da PREMIUM TIMES ta tuntube shi a yau da safe.

Ya dai yi karin hasken cewa wannan tambaya ba shi ne zai amsa ta ba, sai a tuntubi Aminu Iliyasu, wanda shi ne Kakakin Rundunar Sojoji ta 6 da ke Fatakwal.

To amma da PREMIUM TIMES ta tuntubi Kanar Iliyasu, bai bayar da amsa ba, sai ya ce ya na wurin wani taro ne. kuma ba zai iya cewa ga lokacin da zai iya samun sukunin yin magana ba.

GWAMNA WIKE DA MANJO JANAR JAMIL: Kar ta San Kar

An sha yin sa-toka-sa-katsi tsakanin Gwamna Wike da Manjo Janar Sarham, tun daga lokacin da aka nada shi Kwamandan Askarwan Runduna ta 6 cikin Agusta, 2018.

A lokacin zaben 2019, Gwamna Wike ya zarge shi da yi wa dimokradiyya makarkashiya da zagon-kasa a jihar Rivers.

Hakan ya biyo bayan harbe-harben suka tilasta Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) dakatar da tattarawa da bayyana sakamakon zabe.

An kashe akalla sojoji biyu da fararen hula kusan 212 tsakanin watan Fabrairu da Maris a lokutan zaben shugaban kasa da na gwamna.

Ita kan ta INEC ta soki lamirin yadda sojoji suka taka rawa a lokacin zabe a jihar Rivers.

Ranar 9 Ga Mayu, kwanaki kadan kafin zaben gwamna, Sarham ya aargi Wike da kokarin bai wa sojoji cin hanci. Gwamna Wike ya karyata Sarham, har ma ya kai karar Sojojin Najeriya a Kotun Kasa-da-kasa a bisa zargin sun karkashe fararen hula, ji wa wasu raunuka da kuma lalata dukiyoyi, kamar yadda aka yi rikodin a fadin jihar a lokutan zabe.

Share.

game da Author