Gwamnati na da kwararan hujjoji cewa PDP da ‘ya’yanta na yi wa gwamnatin Buhari zagon kasa

0

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnati na da kwararan hujjoji cewa jam’iyyar PDP da wasu daga cikin jiga-jigan ta na yi wa wannan gwamnati zagon kasa don ganin ba ta yi nasara a abin da ta sa a gaba.

Lai Mohammed ya fadi haka ne a wajen taron lakca da aka yi a garin Ilori, jihar Kwara.

Wannan lakca akan yi shi ne duk watan Ramadana inda ake tunatar da musulmai karantarwar addinin musulunci.

” Ina so in tabbatar muku cewa muna da kwararan hujjoji da dama da ya fallasa kulle-kulle da makirci da wasu ‘yan jam’iyyar PDP suke yi wa gwamnatin nan musamman su ga ba a rantsar da gwamnati a ranar 29 ga wata ba.

” Idan ba a manta ba hatta jami’an tsaro sun fito sun bayyana haka cewa sun gano irin wadannan kulle-kulle. Sannan a kwanakin baya har tsame kanta ma’aikatar tsaro ta yi bisa zargin wai akwai rade-radin yi wa Buhari juyin mulki da sojoji ke shiryawa.

Ya kara da cewa tuni har gwamnati sun bankado wasu daga cikin wadannan boyayyun kulle-kulle da ake yin su cikin sirri kuma an jawo hankalin hukumomin tsaron kasar nan domin su kwana cikin shiri.

” Yan adawa na cike da kuncin faduwa zabe kuma suna ta kitsa sharri wajen ganin gwamnati bata iya tsinana komai ba ga talakawan kasar nan.

Lai ya ce gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta bankado sannan ta tona asirin irin wadannan mutane da basu kishi Najeriya.

Limamin babban masallacin Ilori Soliu Orire kira yayi ga mutane da su ji tsoron Allah a al’amurorin su.

Wadanda suka halarci wannan lakca sun hada da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu da sauran gaggan ‘yan siyasa da malamai.

Share.

game da Author