Atiku ya nemi hadimar Buhari ta biya shi diyya ko ya maka ta kotu

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya yi wa Hadimar Kafafen Yada Labarai ta Shugaba Muhammadu Buhari da ta roke shi afuwa,ta cire labara, kuma ta biya shi diyya.

Wannan ya biyo bayan wani labarin da da kwaso ta watsa a kafafen sadarwa na soshiyal midiya, wanda Atiku ya ke ganin ita Lauretta Onochie din ta bata masa suna.

Babban lauyan Atiku, Mike Ozekhome ne ya rubuta mata wasikar a ranar 14 Ga Mayu, inda ya nemi ta karyata labarin da ta watsa, sannan kuma ta biya shi naira milyan 500 diyyar bata masa suna da ta yi.

Ya yi kurarin cewa idan ba ta yi haka ba a cikin kwanaki biyu, to zai maka ta kotu, inda zai nemi ta biya shi diyyar naira biliyan 2.

An rubuta mata wannan wasikar ce mako daya bayan ta watsa wani labari a shafin ta na twitter cewa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta kafa idanun ta a kan wasu al’amurra da Atiku ke yi a kasar da suka jibinci mu’amala da ’yan ta’adda.

Lauretta ta ce Atiku wanda yak an je Dubai domin yin aiki da kuma hutawa, ya na neman hada ’yan ta’adda tun tafiyar sa da ya yi a cikin watan Mayu zuwa Dubai.

Wannan mata dai ta sha watsa labarai na rudu tun bayan da aka nada ta a cikin 2016.

Sannan kuma ta sha yin sa-in-sa ko surfa wa juna munanan kalamai, ita da wadanda ta ke ganin cewa masu sukar Shugaba Muhammadu Buhari ne da gwamnatin sa.

Lauyan Atiku ya ce sharri da karairayin da Lauretta ta gillara wa Atiku sun janyo masa damuwa, zubar da mutunci da kuma yi masa wani kallon mai laifi a idon jama’a.

Daga nan sai aka ba ta kwanaki biyu rak ta cire labarin da ta watsa a shafin ta na twitter ko a maka ta kotu tare da neman biyan diyyar naira bilyan biyu.

PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin ta, an tura mata sakon tes bayan ta ki amsa kira, amma har yau ba ta bada amasa ba.

Share.

game da Author