Masu garkuwa sun kashe malamin jami’a

0

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani malamin jami’a da ke koyarwa a Jami’ar Igbinedion, Okada, cikin Jihar Edo.

Rundunar ’Yan sandan jihar da mahukuntar jami’ar sun tabbatar da kisan malamin mai suna Danmalam Izevbekhai.

Sun ce an bindige shi a kokarin da ya yi na tserewa dga hannun ’yan bindigar, a lokacin da ake nausawa da shi a cikin surkukin jeji.

Al’amarin ya faru jiya Lahadi, kamar yadda NAN ta ruwaito cewa mahara sun datse shataletalen mahadar garin Okada, kan hanyar Benin zuwa Legas.

Mahara sun kama Izevbekahai da sauran fasinjojin da ke cikin motar da ya ke a ciki.

“An ce direban motar ya samu tserewa tare da wasu fasinjoji hudu.” Haka ’yan sanda suka bayyana.

Sun kara da cewa amma wani da shi ma ya yi kokarin tserewar bai yi nasara ba, saboda sun bindige shi.

Malamin dai an bayyana cewa haziki ne kwarai kuma matashi ne da ya kammala jami’ar a cikin 2016, inda ya samu sakamako mafi daraja, wato ‘First Class’.

Wannan ta sa jami’ar ta dauke shi ya na koyarwa.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce sun yi kokari sun kubutar da sauran fasinjojin hudu da suka tsere a cikin daji.

Share.

game da Author