‘Yan Sanda sun kashe Shaho, gogarman masu garkuwa da mutane a titin Abuja-Kaduna

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar bindige babban gogarman masu garkuwa da mutane, wanda ya yi garkuwa da Shugaban Hukumar Gudanarwar UBEC, a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

An bindige shi a wani bata-kashi da aka yi da mahara da ‘yan sanda a cikin dajin Rijana, cikin Karamar Hukumar Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin ’Yan Sanda na Kasa, Frank Mba ne ya bayyana haka jiya Lahadi, inda ya bayyana sunan dan bindigar da Sumaila Sule, da aka fi sani da suna Shaho, kuma an ce dan cikin kauyen Rijana ne.

Rijana na kan Titin Abuja idan an bar Kaduna ba da nisa ba.

Jami’an tsaro sun bayyana shi cewa kuntukurmin dan fashi da kuma garkuwa da mutane ne, wanda suka dade sun a nema ruwa a jallo.

Sule Shaho ya dade shi da gungun yaran sa su na fashi da kuma garkuwa da mutane a cikin Jihar Kaduna da kewaye.

Mba ya ce Shaho ya mutu a jijjifin asubahin ranar Asabar, bayan ya samu raunukan harbin bindigar da ‘yan sandan ‘Operation Puff Adder’ suka yi masa.

PREMIUM TIMES ta bada labarain yadda aka yi garkuwa da Shugaban UBEC, Mahmod Abubakar shi da ‘yar sa da kuma yadda suka samu kubuta a cikin watan Afrilu.

Har direban sa aka bindige har lahira kafin a gudu da shi da ‘yar ta sa, a ranar 17 Ga Afrilu, kusa da garin Rijana.

Bayan Shaho ya sha harbin bindiga, ‘yan sanda sun garzaya da shi asibiti inda ya karasa a can.

“Sai dai kuma wani bayanin sirri da jami’an tsaron suka samu daga bakin Shaho kafin mutuwar sa, ya sa a ranakun 18 da 19 Ga Mayu sun gudanar da kame a wasu wurare, har suka yi nasarar kama wasu yaran Shaho su hudu, kuma aka samu bindigogi samfurin AK 47 a hannun su.”

Sun ce cikin su akwai Musa Hassan, Umar Ya’u, Umar Musa da kuma Muhammad Sani, dukkan su ’yan cikin Rijana, da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Share.

game da Author