A zaman kotun da ke sauraren shari’ar zaben kujerar Sanata ta Kaduna ta tsakiya, wakilan jam’iyyar PDP 9 ne suka bada shida a zauren kotun.
Dan takarar kujerar sanatan Kaduna ta Tsakiya na jam’iyyar PDP Lawal Adamu ya garzaya kotun domin kalubalantar nasarar da Uba Sani na Jam’iyyar APC yayi a Zaben.
PDP ta ce anyi aringizon kuri’u a mazabu da dama a a zaben sanatan a Kaduna.
Wadanda suka bada shaida sun ce a mazabun da suka yi aiki da ya hada da mazabar Magajin Gari da ke karamar hukumar Birnin Gwari.
Sun bayyana cewa aringizon da aka yi baya misaltuwa domin har da jami’an tsaro ake hada baki wajen dankare akwatinan zabe da kuri’un karya.
Baya ga wadannan mutane tara da suka bada shaida, Adamu ya ce akwai wasu mutanen har 96 da zasu bayyana a gaban kotun domin bada shaida da kuma fadi wa kotu irin yadda rika aringizon zabe da canja kuri’u a mazabun kananan hukumomi shida suka yi shiyyar Kaduna ta tsakiya.