Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kashe naira biliyan 35 wajen samar da kayan aiki da alawus-alawus ga jami’an tsaro da kuma tallafawa ga wadanda hare-haren Zamfara ya shafa.
Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ne ya bayyana haka a jiya Talata, a Gusau, babban birnin jihar, a lokacin da ake rabon kayan agaji ga wadanda hare-hare suka shafa.
Shinkafi ya ce kayan agajin Uwargidan Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ce ta bayar da tallafin su.
Ya gode wa Aisha Buhari game da kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya ce tun da wannan fitina ta barke, gwamnatin jihar ba ta sassauta kokarin ta wajen bada hadin kai da goyon baya da taimako ba ga jami’an tsaro.
Ya ce ta na haka ne domin ganin an kawo karshen wannan fitintinu da suka afka wa Jihar Zamfara.
Ya ce sun bayar da ofis na kwatankwacin naira milyan 10 ga Sojojin Najeriya.
“Mun dade mu na goyon bayan jam’an tsaro wajen samar musu kayan aiki da alawus da kudin su ya haura sama da naira bilyan 20.
“Mun sai wa jami’an tsaro sabbin Hilux 570 da Range Rover Ford domin samun saukin gudanar da sintiri.
Shin kafi ya yi karin bayani da cewa Gwamna Abdul’aziz Yari ya kafa Kwamitin Tantance Barna Da Bayar Da Agaji, wanda Kakakin Majalisar Dokoki, Sanusi Rikiji ke shugabanta.
Kwamitin inji shi zai taimaka wa wadanda mahara suka kassara.
An kasa aikin kwamitin hawan-hawa, ta yadda za a tallafa wa wasu da naira 500,000 wasu kuma naira 250,00 ga duk wanda aka ji wa ciwo mutum daya.
Kwamitin kuma ya rika tallafa wa da naira 250, 000 ga duk wanda ya yi asarar dukiya gida ko rumbu. Ya ce an kashe naira bilyan 5 a wannan fanni.
“Har zuwa 2013 sojoji 27 kadai ne a Jihar Zamfara, amma a yanzu akwai kimanin sojoji 4,000.”
Saboda haka ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa bisa rawar ganin da suka yi wajen kokarin nganin an kakkabe mahara domin samun zaman lafiya a Zamfara.
A na sa jawabin, Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Zamfara, Sanusi Kwatarkwashi, ya ce akalla akwai mazauna sansanonin gudun hijira har 37,000 da aka yi wa rajista a jihar.
Ya ce sun hada da maza 3,634, mata 9,269 sai kuma kananan yara 23,172.
Ya ce daga Nuwamba 2018 zuwa yanzu an kashe mutane 586, an raunata 267 sannan kuma an yi garkuwa da 338.
“A wannan dan lokaci, an kona rumbuna, an lalata gonaki na milyoyin nairori kuma an sace dimbin shanu da tumakai ko kuma na karkashe su.”
A karshe ya ce adadin zai iya haura haka, domin akwai wadanda idan an kai musu harin ba su kawo rahoto.