Babu wani dan PDP da zai shugabanci kwamiti a majalisar Tarayya – Inji Oshiomhole

0

Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana cewa babu wani dan jam’iyyar adawa ta PDP da zai shugabanci wani kwamiti a majalisar Tarayya a wannan karon.

Oshiomhole ya bayyana haka ne a taron ganawa da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi da zababbun ‘yan majalisar Tarayya na jam’iyyar APC a fadar gwamnati ranar Talata.

” Mun yi kuskure a 2015 wajen zaben shugabanni, amma ba za muyi wannan kuskure ba yanzu. Zababbun ‘yan jam’iyyar mu ne za su rike manyan mukamai a majalisa. Babu wani dan jam’iyyar adawa da zai rike kujerar shugabancin majalisa ko da ko guda daya ne.

” Da ‘yan Najeriya na son su da sun zabe su wato PDP din. Kuma ida ba a manta ba a zamanin da suka sheke ayar su ay sune suke raba wa kansu kujerun shugbancin na kwamitin majalisa.

” Da dadaddun ‘yan majalisa da sabbi duk za a nada su shugabannin kwamitoci. Kowa zai samu abu a majalisar.

Share.

game da Author