GUMURZU: An kashe Boko Haram 39, sojoji 20 sun jikkata

0

Rundunar Kasa-da-kasa ta Sojojin MNJTF ta bayyana cewa ta kashe ’yan Boko Haram 39, tare da kwace makamai masu tarin yawa daga hannun su.

Sai dai kuma sanarwar ta ce an raunata sojoji 20 a wurin fafata yakin.

Sojojin MNJTF hadin-guiwar sojoji ne tsakanin kasashen Najeriya, Chad, Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar.

An kafa rundunar ce musamman domin dakile hare-haren Boko Haram a kasashen hudu masu makwabtaka da juna.

Kakakin rundunar mai suna Timothy Anthigha, ya tabbatar da cewa kafsa yakin, a cikin wata samarwa da ya fitar ga manema labarai Jiya Laraba a Abuja.

Kanar Anthigha ya ce an kashe Boko Haram 39 lokacin da suka yi yunkurin kai wa sojoji hari a Cross Kaura, shekaranjiya Talata.

Ya ce an kwashe dukkan sojojin da aka ji wa ciwo an garzaya da su inda ake kulawa da su kuma ake ba su magunguna.

Shekara goma kenan ana fafata yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabacin Najeriya.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta sha nanata cewa an gama da Boko Haram, amma kuma a kullum ba su daina kai hare-hare ba.

Sai dai kuma akasarin hare-haren na su ya tsaya ne a jihohin Barno da Yobe kawai.

Share.

game da Author