KASHE-KASHEN ZAMFARA: Sojoji sun damke Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Anka

0

Sojojin Rundunar “Operation Sharan Daji” a Zamfara, sun bada sanarwar damke Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Anka, Yahuza Wuya.

Ana zargin Yahuza ne da hannu wajen mara wa ’yan bindiga baya. An ce ya na da alaka da su.

Jami’in Yada Labarai na Sojojin na Riko, Clement Abiade ya tabbatar da haka a wata sanarwar da ya fitar ga manema labarai a yau Alhamis.

Ya ce an kama mataimakin shugaban karamar hukumar ta Anka, tun a ranar 13 Ga Afrilu, bayan an samu ingantaccen bayanin alakar sa da mahara a kauyukan Wuya da Sanke.

Abiade ya yi zargin cewa Yahaya na taimakawa wajen sayar musu da shanun da mahara suka yi fashi, kuma ya na ba mahara kwarmaton duk halin da sojoji da sauran jami’an tsaro ke ciki.

Kakakin Sojoji ya ci gaba da cewa “Yahaya ya taimaka wajen tserewar da wani rikakken dillalin bindigogi mai suna Sani Yaro ya yi daga kurkukun Gusau.”

A wata sabuwa kuma, Abiade ya bayyana cewa sojoji sun kama wasu masu kwarmata wa mahara bayanai a kan hanyar kauyen Burukusuma zuwa Sabon Birni a cikin Jihar Sokoto.

Wadanda aka kama din su ne Ibrahim Bangaje da wani mai suna Ado Bayero.

Ya ce za a gaggauta mika su ga jami’an tsaron da suka dace domin gurfanar da su.

Share.

game da Author