Buhari ya umarci ministoci su mika ayyukan su na shekaru hudu

0

Yayin da wa’adin zangon Shugaba Muhammadu Buhari na farko ya zo karshe, ya bada umarnin cewa kowane minista ya gaggauta mika cikakken bayanin ayyuka da tsare-tsaren da ya gunanar.

Wannan ya shafi ministoci, hukumomin da sauran bangarorin ayyukan gwamnati.

An ba su wa’asin mako daya, wato daga nan zuwa ranar 24 Ga Afrilu, kowa ya mika na sa rahoton.

An bukaci kowanen su ya mika na sa rahoton Kwamitin Shugaban Kasa Mai Bin Diddigin Ayyuka da ke ofishin Mataimakin Shugaban Kasa.

Wannan bayani ya fito ne daga Babban Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu.

Shi ma Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya fitar da irin wannan sanarwa cewa Ministoci su tabbatar da cewa duk wasu sauran takardun ayyukan da ba su gabatar ba, to su gaggauta mika bayana su a Ofishin Sakataren Gwamnati nan da ranar 30 Ga Mayu, 2019.

Sanarwar ta kara da cewa an dage taron Majalisar Zartaswa na 9, da na 10, da aka tsara yi ranar Alhamis 25 Ga Afrilu da 2 Ga Mayu, saboda bikin ranar Ma’aikata da a gudanar 1 Ga Mayu, 2019.

Share.

game da Author